Ban janye takarar Gwamnan Jihar Legas ba - Olusola Sanwo-Olu

Ban janye takarar Gwamnan Jihar Legas ba - Olusola Sanwo-Olu

Mun samu labari cewa Mista Babajide Olusola Sanwo-Olu wanda ya sha alwashin tika Gwamnan Jihar Legas Akinwumi Ambode a Jam’iyyar APC mai mulki ya bayyana cewa bai fasa takara ba.

Ban janye takarar Gwamnan Jihar Legas ba - Olusola Sanwo-Olu

Babajide Olusola Sanwo-Olu ya rantse sai yayi takara da Ambode
Source: UGC

A cikin ‘yan kwanakin nan ne aka far yada labari cewa Olusola Sanwo-Olu ya fasa fitowa takarar Gwamna kamar yadda yayi niyya. ‘Dan takarar na Jam’iyyar APC yace babu gaskiya a wannan labari da ake ta yadawa ko ta ina.

Babajide Olusola Sanwo-Olu ya fitar da jawabi na musamman ta bakin kwamitin yakin neman zaben sa cewa maganar fitowar sa takarar Gwamna na nan daram-dam-dam. Tuni dai har ‘Dan takarar Gwamnan ya yanki fam a Jam'iyyar APC.

KU KARANTA: Buhari ya sa baki cikin rikicin Ambode da Tinubu

Ana tunani cewa Tsohon Gwamnan Legas Bola Tinubu ne yake marawa Sanwo-Olu baya. Sai dai Sanwo-Olu ya musanya hakan inda yace ya isa ya tsaya da kafafun sa. ‘Dan takarar yace duk abin da ake nema na zama Gwamna yana da shi.

Mista Sanwo-Olu ya rike Kwamishina kusan sau 3 a Jihar Legas ban da kuma mukamai iri-iri da ya rike. Yanzu haka dai ‘Dan takarar yana cikin Gwamnatin Ambode. ‘Dan takarar mai shekaru 53 yana da goyon bayan manyan APC a Legas.

A makon nan ne Gwaman Legas Akinwumi Ambode ya karyata rade-radin cewa akwai kwantacciyar rigima tsakanin sa da Mai gidan sa Asiwaju Bola Tinubu inda yace babu abin da ya shiga tsakani su.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel