Gwamnan Osun ya fara biyan Ma’aikata albashi bayan shekaru 3

Gwamnan Osun ya fara biyan Ma’aikata albashi bayan shekaru 3

Mun samu labari cewa Gwamnatin Jihar Osun ta fara biyan Ma’aikatan ta cikakken albashin su kamar yadda ya dace. Yanzu dai kowane Ma’aikacin Jihar yana tashi da albashin sa ba tare da an rage ko sisi ba kamar yadda aka saba.

Gwamnan Osun ya fara biyan Ma’aikata albashi bayan shekaru 3

Ma'aikatan Jihar Osun sun fara karban cikakken albashin su a karon farko tun 2015
Source: Twitter

Kwamishinan yada labarai na Osun Adelani Baderinwa ya bayyanaw a’Yan jarida cewa Gwamnan Jihar ya soma biyan kaf Ma’ikatan Jihar albashin su. Kwamishinan yace an fara biyan su kudin su ne tun a Watan Yulin nan.

Tun a tsakiyar 2015 ne Gwamna Rauf Aregbesola ya fara zaftarewa Ma’aikatan Jihar albashi bayan ya shiga matsin tattali. Yanzu dai an yi nasara kowa na daukar abin da ya kamata ya samu a karshen wata inji Kwamishinan Jihar.

KU KARANTA: Sanatan da ya saba tika rawa a Majalisa ya samu tutar takarar Gwamnan Osun

Shekaru kusan 3 kenan aka yi Ma’aikatan Osun su na shan wahala kafin abubuwa su dawo daidai watanni uku da su ka wuce. Manyan Ma’aikata dai na samun kashi 50% zuwa kashi 75% na albashin su ne a Gwamnatin nan.

Kwamishinan ya nuna cewa halin tattalin arzikin da Jihar Osun ta fada ne ya sa aka ragewa ma’aikata albashi. Gwamnatin Jihar ta alakanta wahalar da aka shiga da karyewar gangar danyen mai a kasuwar Duniya a 2015.

Kwanan nan ne Gwamnatin Tarayya ta maidowa Jihar ta Osun wasu kudi da ta ke bi bashi har Naira Biliyan 16.6. Da wannan kudi ne Jihar ta kara tayi amfani wajen biyan bashin albashi da fansho da kudin Ma’aikatan da su ka makale.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel