Najeriya ta shiga hannun tsira – Inji Oshiomhole yayinda ya taya sabon shugaban DSS murna

Najeriya ta shiga hannun tsira – Inji Oshiomhole yayinda ya taya sabon shugaban DSS murna

- Shugaban APC na kasa ya taya Yusuf Bichi murna akan nada shi shugaban hukumar SSS

- Oshiomhole yace a yanzu Najeriya zat samu cikakkiyar kulawa

Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole ya taya Yusuf Bichi murna akan nada shi shugaban hukumar SSS da shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi.

Duk da Allah wadai da aka yi akan nadin da shugaban kasar yayi, Oshiomhole ya bayyana a wasikar taya murnarsa zuwa ga bichi cewa Najeriya a matsayin kasa, zata kasance cikin cikakkiyar kulawa muddin tana a karkashin sabon shugaban.

Najeriya ta shiga hannun tsira – Inji Oshiomhole yayinda ya taya sabon shugaban DSS murna

Najeriya ta shiga hannun tsira – Inji Oshiomhole yayinda ya taya sabon shugaban DSS murna
Source: Depositphotos

Oshiomhole ya bayyana a shafinsa na tweeter a ranar Juma’a, 14 ga watan Satumba cewa: “ina taya sabon shugaban DSS Yusuf Magaji Bichi murna akan nada shi da mai girma, shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi. Najeriya zata kasace cikin kulawa.”

KU KARANTA KUMA: Na hada kai da wani malamin tsubbu don muyi kudi da mai koyon aiki a wurina – Mai magani

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a ranar Alhamis, 13 ga watan Satumba, ya bayyana Yusuf Magaji Bichi a matsayin sabon darakta-janar na hukumar yan sandan farin kaya (DSS).

Sabon shugaban zai karbi aiki daga hannun Matthew Seiyeifa, wanda yam aye gurbin Lawal Daura da aka dakatar.

Garba Shehu, kakakin shugaban kasa ne ya bayar da sanarwar a wani jawabi da ya saki.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel