An kashe mutane 11 yayinda aka raunata 21 a sabon harin Zamfara

An kashe mutane 11 yayinda aka raunata 21 a sabon harin Zamfara

An tabbatar da mutuwar mutane 11 a lokacin wani hari da aka kai wata cibiyar kallo a jihar Zamfara a safiyar ranar Alhamis, 13 ga watan Satumba, jaridar Premium Times ta ruwaito.

Cibiyoyin kallon sun kasance wurare masu zaman kansu da mutane ke taruwa domin kallon wasannin kwallo da fina-finai. Akwai irinsu da dama a fadin Najeriya.

Koda dai yan sanda sun ce gawawwakin mutane shida aka gano, kakakin gwamnan jihar, Ibrahim Dosara ya tabbatar wa da majiyarmu ta Premium Times cewa mutane 11 ne suka mutu.

An kashe mutane 11 yayinda aka raunata 21 a sabon harin Zamfara

An kashe mutane 11 yayinda aka raunata 21 a sabon harin Zamfara
Source: Depositphotos

“Mutane 11 aka kashe sannan aka raunata 21 a lamarin ya afku yankin karamar hukumar Shinkafi na jihar Zamfara,” inji Dosara.

Yace bincike ya nuna cewa barayin shanu ne suka kai hari, amma ana nan ana cigaba bincike.

KU KARANTA KUMA: Na hada kai da wani malamin tsubbu don muyi kudi da mai koyon aiki a wurina – Mai magani

Da suke tabbatar da lamarin yan sanda sun bayyana cewa mutane shida ne suka mutu yayinda 10 suka cikkata.

Kakakin yan sandan jihar, Mohammed Shehu, wanda ya tabbatar da harin a wata sanarwa yace bayan samun kira daga yankin, tura jami’anyan sanda da sojoji yankin.

A cewarsa, jami’an sunyi arangama da yan fashin sannan suka tursasa su guduwa cikin daji.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel