Da alama Gwamnatin Buhari ba ta da niyyar kara albashin Ma’aikata - Shugaban SSANU

Da alama Gwamnatin Buhari ba ta da niyyar kara albashin Ma’aikata - Shugaban SSANU

Mun samu labari cewa Kungiyar Ma’aikatan Jami’a a Najeriya watau SSANU sun ja kunnen Gwamnatin Tarayya game da kwan-gaba-kwan bayan da ta ke yi game da maganar karin albashi a Kasar nan.

Da alama Gwamnatin Buhari ba ta da niyyar kara albashin Ma’aikata - Shugaban SSANU

SSANU ta nemi Gwamnatin Buhari tayi maza ta kara albashin Ma'aikata
Source: Twitter

Kungiyar SSANU watau “Senior Staff Association of Nigerian Universities” ta bayyanawa Gwamnatin Najeriya cewa idan ba tayi maza ta dauki mataki game da shirin karawa Ma’aikata albashi ba za ta dauki matakin da duk ba za a ji dadi ba.

Shugaban Kungiyar Kwamared Samson Chijioke Ugwoke ya bayyana cewa Gwamnatin Buhari ba ta da niyyar karawa Ma’aikatan Gwamnati albashi bayan tayi wa mutane alkawarin hakan a baya. SSANU tace ta gaji da wannan alkawari na bogi.

KU KARANTA: Gwamnatin Tarayya tayi karin haske game da shirin N-Power

Chijioke Ugwoke yace idan aka zo maganar kashe kudi wajen zabe Gwamnati ta iya sakin kudi sai dai kuma da zarar an fara batun karawa Ma’aikata albashi sai labari ya canza. Shugaban ma SSANU ya kuma nemi a sake duba harkar tsaron kasar.

Kungiyar ta SSANU ta kuma yi tir da makudan kudin da masu rike da mukaman Gwamnati su ke kashewa da sunan kudin tsaro. Chijioke Ugwoke yace wannan dabi’ar banza ce da ke neman zama barazana ga tsarin siyasar Najeriya da ya kamata a duba.

Samson Chijioke Ugwoke yayi wannan bayani ne wajen wani babban taron SSANU da aka yi a Jami’ar Jihar Delta da ke Garin Abraka. A karshe, Shugaban Kungiyar ya nemi ayi zaben 2019 cikin kwanciyar hankali ba tare da tada wata fitina ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel