Mabanbantan ra'ayoyin 'yan Najeriya game da takarar da PDP ta ba Atiku

Mabanbantan ra'ayoyin 'yan Najeriya game da takarar da PDP ta ba Atiku

Labarin da muke samu da dumin sa yanzu na nuni ne da cewa tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya Alhaji Atiku Abubakar ne ke kan gaba yayin da aka soma kirga kuri'un da aka kada na zaben fitar da gwanin jam'iyyar PDP.

Kamar yadda muka samu, Atiku Abubakar din yayiwa gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal fintikau wanda hakan ne ya bashi damar lashe zaben.

Mabanbantan ra'ayoyin 'yan Najeriya game da takarar da PDP ta ba Atiku

Mabanbantan ra'ayoyin 'yan Najeriya game da takarar da PDP ta ba Atiku
Source: Twitter

KU KARANTA: Gwamnan Zamfara na shirin fita daga APC

Legit.ng ta samu cewa yanzu dai biyo bayan lashe wannan zaben, Atiku Abubakar ne zai kara da shugaba Buhari na APC a zaben 2019 mai zuwa.

Tuni ne kuma 'yan Najeriya da dama suka soma bayyana ra'ayoyin su game da takarar ta shugaban kasa Muhammadu Buhari da Atiku Abubakar.

Yayin da wasu ke ganin cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari kawai ya kwantar da hankalin sa domin ya riga ya lashe zaben, wasu kuma na ganin Atiku ne zai yi nasara a zaben na 2019.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel