APC ta rasa shugabancin Majalisun Najeriya bayan Dogara ya tsere

APC ta rasa shugabancin Majalisun Najeriya bayan Dogara ya tsere

A halin yanzu, Jam’iyyar APC mai mulki ta rasa gaba daya shugabancin Majalisun Tarayyar Najeriya bayan da Shugaban Majalisar Wakilai na kasar Rt. Hon. Yakubu Dogara ya koma PDP.

APC ta rasa shugabancin Majalisun Najeriya bayan Dogara ya tsere

Yakubu Dogara ya bi Saraki zuwa Jam’iyyar adawa ta PDP
Source: Twitter

A jiya ne Shugaban Majalisar Wakilai ya bi Takwaran sa Bukola Saraki zuwa PDP. Dogara ya sanar da ficewar sa daga APC ne ta bakin wani babban Hadimin sa Turaki Hassan. Dogara yace APC ba addini ba ce da za ayi riko da ita.

Yakubu Dogara ya tsere daga APC zuwa Jam'iyyar PDP ne bayan da wasu ‘Yan Mazabar sa ta Bogoro/Dass/Tafawa Balewa su ka saya masa fam din takara a karkashin Jam’iyyar PDP su na rokon sa alfarma yayi watsi da APC ya huta.

KU KARANTA: An maka Shugaban Majalisar Dattawa Saraki kara a Kotu

Mohammed Aminu Tukur, Adamu Jambil da kuma Amina Saleh ne su ka sayawa Shugaban Majalisar fam din PDP. Dogara yace su ne su ka kafa APC kuma dole ta sa ya bar ta saboda tsantsar rashin adalcin da ake yi masu a tafiyar Jam’iyyar.

‘Dan Majalisar yace su ne mutanen farko da su ka fara karbar APC a Bauchi amma yanzu ya canza gari saboda Jam’iyyar ta gaza cika alkwarin da ta dauka sai dais hara karya. Dogara yace Jihar Bauchi baya ta ke ci a mulkin na APC.

Ita dai Jam’iyyar APC mai mulki ta maida martani inda ta bayyana cewa Yakubu Dogara zai sha mamaki a zaben 2019 tace dama can ba ta yi mamakin jin cewa Shugaban Majalisar ya bar APC ba domin ta fahimci take-taken sa tun fil-azal.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel