Shugabannin kudu sun ki amincewa da sabon shugaban DSS, sun zargi Buhari da kabilanci

Shugabannin kudu sun ki amincewa da sabon shugaban DSS, sun zargi Buhari da kabilanci

- Shugabannin kudu sun nuna rashin amincewarsu da sabon shugaban hukumar DSS da Buhari ya nada

- Sun ce ba'a taba samun shugaban kasa mai kabilanci kamar na Buhari ba a tarihin kasar

- Dattawan sun ce shugaban kasar na sake raba kan Najeriya

Wasu dattawan yankin kudu sun zargi Shugaban kasa Muhammadu Buhari da sake raba kan Najeriya fiye da duk wani shugaban kasa a tarihi.

A wata sanarwa da aka saki a ranar Alhamis, 14 ga watan Satumba, kungiyar tayi Allah wadai da tsige Matthew Seiyefa, mukaddashin darakta janar na hukumar yan sandan farin kaya (DSS).

Shugabannin kudu sun ki amincewa da sabon shugaban DSS, sun zargi Buhari da kabilanci

Shugabannin kudu sun ki amincewa da sabon shugaban DSS, sun zargi Buhari da kabilanci
Source: Depositphotos

Shugabannin sun yi zargin cewa wannan abu da yayi ya nuna cewa “bai yi amanna da Najeriya a matsayin tsinsiya madaurinki daya ba.”

An daura Seyefa a matsayin shugaban rikon kwarya bayan an dakatar da Lawal Daura, tsohon shugaban DSS kan mamayar da jami’ansa suka kai majalisar dokokin kasar.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a ranar Alhamis, 13 ga watan Satumba, ya bayyana Yusuf Magaji Bichi a matsayin sabon darakta-janar na hukumar yan sandan farin kaya (DSS).

KU KARANTA KUMA: An cafke wani matashi yayin da yake lalata allon takarar Buhari (hotuna)

Sabon shugaban zai karbi aiki daga hannun Matthew Seiyeifa, wanda yam aye gurbin Lawal Daura da aka dakatar.

Garba Shehu, kakakin shugaban kasa ne ya bayar da sanarwar a wani jawabi da ya saki.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel