Wani Sanata ya bukaci kotu ta aika Saraki gidan yari

Wani Sanata ya bukaci kotu ta aika Saraki gidan yari

- Sanata Omo-Agege mai wakiltan Delta ta tsakiya ya nemi kotu ta garkame shugaban majalisa, Bukola Saraki

- Omo-Agege ya yi wannan karar ne saboda wai Saraki ya hana a biya shi albashinsa da bai karba ba lokacin da aka dakatar dashi ba bisa ka'ida ba

- Omo-Agege ya nemi kotun ta gayyaci Saraki ya bayyana dalilin da yasa yaki bin umurnin kotun ko kuma a jefa shi a kurkuku

Wani Sanata ya bukaci kotu ta aika Saraki gidan yari
Wani Sanata ya bukaci kotu ta aika Saraki gidan yari
Source: Twitter

A yau, Alhamis ne Sanata Ovie Omo-Agege mai wakiltan Delta ta tsakiya ya bukaci babban kotun tarayya da ke Abuja ta jefa Shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki a kurkuku saboda kin biyaya ga umurnin kotu.

A kara da ya shigar a kotun, Omo-Agege ya yi ikirarin cewa Saraki ya yi watsi da umurnin da kotu ta bayar na soke dakatarwar da aka yi masa daga majalisar dattawa saboda ya shigar da majalisar kara a kotu.

DUBA WANNAN: APC ta bayyana abinda zai faru da Dogara idan ya koma PDP

Lauyan Omo-Agege, Dr Alex Iziyon, SAN, ya shaidawa kotu duk da cewa wanda ya ke karewa ya fara zuwa aiki a majalisa tun bayan da kotu ta soke dakatarwa da akayi masa a ranar 10 ga watan Mayu, Saraki ya ki amincewa a biyansa hakokinsa.

"Wanda na ke karewa ya koma bakin aiki amma ba'a biya shi hakokinsa ba. Hakan yasa muke son wannan kotun ta gayyaci wanda akai kara domin su fadi dalilin da zai hana a jefa su kurkuku saboda kin biyaya ga hukuncin kotu," Inji Iziyon, SAN.

Ya kuma nemi kotun ta bashi izinin aike wa majalisar dattawa da Saraki sammaci ba tare da ya yi ido biyu da su ba.

Alkalin da ke Shari'ar, Justice Nnamdi Dimgba, ya ce kotun za ta sanar da ranar da za'a saurari karar nan ba da dadewa ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel