Dalilin da ya sa na dare kololuwar tsanin kafa na’urar wayar tafi da gidan ka – Iliyasu

Dalilin da ya sa na dare kololuwar tsanin kafa na’urar wayar tafi da gidan ka – Iliyasu

A ranar Laraba, 12 ga watan Satumba da rana ne wani matashi dan shekara 28 Nurudeen Iliyasu ya haye kololuwar tsanin da ake kafa na’urar wayar tafi da gidanka domin nuna fushin sa ga durkushewar tattalin arzikin kasar.

Iliyasu ya dare wannan tsani ne a garin Abuja dauke da wasu rubuce rubucen da ke nuna bacin ran sa ga yadda al’amura ke gudana a kasar nan.

Iliyasu ya bayyana cewa zai zauna a kan wannan tsani na kwanaki bakwai sannan ba zai damu ba koda zai rasa ran sa ne.

Dalilin da ya sa na dare kololuwar tsanin kafa na’urar wayar tafi da gidan ka – Iliyasu

Dalilin da ya sa na dare kololuwar tsanin kafa na’urar wayar tafi da gidan ka – Iliyasu
Source: Facebook

Yace: “Koma bayan tattalin arzikin da muke fama da shi a kasar nan ya hana mutane sakat. An wayi gari mutane da dama basu iya ci abinci saboda talauci, rashin aikin yi, rashin samun ababen more rayuwa da sauran su.

“Burina za ta cika idan har na mutu a nan idan dai hakan zai kawo canji a kasar nan."

KU KARANTA KUMA: Rayuwana da na iyalina na cikin hatsari - Atiku

Bayan haka likitoci sun bayyana cewa Iliyasu zai iya rayuwa na tsawon wasu ‘yan kwanaki idan yana shan ruwa kadai.

A karshe mai gadin wannan tsani Ayuba Luka ya bayyana cewa a wannan rana Iliyasu ya nemi izinin sa domin ya dare wannan tsani ammm ya ki amincewa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel