Dan takarar gwamna a jam'iyyar adawa ya lissafa mutum 2 da ba barayi ba a gwamnatin Buhari

Dan takarar gwamna a jam'iyyar adawa ya lissafa mutum 2 da ba barayi ba a gwamnatin Buhari

- Dan takarar gwamna ya lissafa wadanda ba barayi ba a gwamnatin Buhari

- Sunan dan takarar Sheikh Badaru Kano

- Yace daga shi shugaba Buhari din sai kuma Hamid Ali ne kadai tsarkakku

Shehin malamin addinin musulunci kuma dan siyasa dake neman zama gwamnan jihar Kano a jam'iyyar adwa ta Green Party of Nigeria, GPN mai suna Sheikh Badaru Kano ya lissafa mutum biyu kacal da yace su kadai ne ba baryi ba a gwamnatin shugaba Buhari.

Dan takarar gwamna a jam'iyyar adawa ya lissafa mutum 2 da ba barayi ba a gwamnatin Buhari

Dan takarar gwamna a jam'iyyar adawa ya lissafa mutum 2 da ba barayi ba a gwamnatin Buhari
Source: Depositphotos

KU KARANTA: Wata 'yar arewa ta samu babban mukamin kasa-da-kasa

Sheikh Badaru dai ya yi wannan ikirarin ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai kamar dai yadda majiyar mu ta Rariya ta ruwaito inda yace daga shi shugaba Buhari din sai kuma Hamid Ali ne kadai tsarkakku.

Legit.ng ta samu cewa haka zalika Sheikh din ya kara da cewa ba wai lallai kawai Lawal Daura bane barawo a gwamnatin Buhari domin kuwa akwai su da yawan gaske.

A wani labarin kuma, Mataimaki na musamman akan harkokin cikin gida ga tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan lokacin mulkin sa mai suna Dakta Waripamo-Owei Dudafa, a jiya ya kara jadda cewa shi fa dukkan kudaden da ake bincikar sa da ci, sa shi akayi.

Dakta Waripamo-Owei Dudafa ya bayyana cewa tsohon shugaban kasar Dakta Goodluck Jonathan da matar sa Patience Goodluck sune suka sa shi ya cire kudaden kuma yana ganin ya kamata ayi masa adalci.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel