Gwamnoni 6 da zasu tsaya takarar kujeran majalisar dattawa a 2019

Gwamnoni 6 da zasu tsaya takarar kujeran majalisar dattawa a 2019

Kamar ya zama ruwan dare, gwamnonin Najeriya sun mayar da majalisar dattawan Najeriya wajen share zangon rayuwarsu tun kundin tsarin mulkin Najeriya bai bada iyakan shekarun da mutum zai iya takara ba.

Kamar kullun, kimanin dukkan gwamnonin da wa’adinsu na shekara takwas a matsayin gwamnoni a jihohinsu, sun bayyana niyyar komawa majalisar dattawan tarayya.

Ga jerin gwamnonin da suka bayyana niyyar takarar kujeran Sanata a 2019:

1. Gwamnan jihar Zamfara, AbdulAziz Yari

Gwamnan jihar Zamfara kuma shugaban gamayyar gwamonin Najeriya, Abdulaziz Yari, ya bayyana niyyar kawarda tsohon gwamnan jihar, Alhaji Sani Yarima, daga kujerar Sanata mai wakilan mazabarsu. Amma kafin muhawara yayi nisa, Sanata Yarima ya bayyana cewa ya hakura kuma ya yafewa Yari kujeran.

2. Gwamnan jihar Yobe, Ibrahim Geidam

Duk da mazabarsa daya da tsohon gwamnan jihar, Bukar Abba Ibrahim, gwamnan jihar Yoben ya alanta niyyar kawar da maigidansa a zaben 2019. Shi kuma Bukar Abba, ya jaddada niyyar cigaba da zama a majalisar

KU KARANTA: Buhari ya sa baki cikin rikicin Tinubu da gwamnan jihar Legas, Ambode

3. Gwamnan jihar Nasarawa, Tanko AlMakura

Kamar sauran dai, Gwamnan jihar Nasarawa, Tanko AlMakura, ya alanta niyyar komawa majalisar dattawan tarayya domin cigaba da rayuwar siyasarsa.

4. Gwamnan jihar Kwara, Abdul Fatah Ahmed

Bayan komawarsa jam’iyyar PDP daga APC tare da maigidansa, Bukola Saraki, Abdul Fatah Ahmed, ya alanta niyyar takara kujeran Sanata mai wakiltan mazabar Kwara ta kudu.

5. Ajibola Ajimobi, gwamnan jihar Oyo

Duk da cewa ya yi alkawarin cewa ba zai sake takara kujeran siyasa ba a rayuwarsa, gwamnan Ajibol Ajimobi, ya saba alkawarinsa bayan ya bayyana niyyar takarar kujeran majalisan dattawa.

6. Gwamnan jihar Ogun, Ibukunle Amosun

Duk da cewan ya taba zama Sanata kafin yanzu, jam’iyyar APC a jihar ta zabshi a matsayin wanda zai wakilci Ogun ta tsakiya.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel