Buhari ya sa baki cikin rikicin Tinubu da gwamnan jihar Legas, Ambode

Buhari ya sa baki cikin rikicin Tinubu da gwamnan jihar Legas, Ambode

Dubi ga yadda takun saka tsakanin babba jigon jam’iyyar All Progressives Congress, Bola Tinubu, yarons kuma gwamnan jihar Legas, Akinwumi Ambode, ke kokarin kawo cikas ga nasaran jam’iyyar a jihar a zaben bana. Shugaba Buhari ya gayyaci Tinubu fadar shugaban kasa, Abuja.

Legit.ng ta kawo muku rahoton cewa rikici ya kunno kai tsakanin Ambode da maigidansa kuma hakan zai iya hana jam’iyyar APC samu nasara a jihar Legas a zaben 2019.

Duk da cewa dukkansu biyu sun musanta takun saka tsakaninsu, gamayyar gwamnonin APC sun bukaci Buhari da ya tayasu rokon Tinubu kada ya kunyata takwararsu, Ambode.

Amma kakakin Tinubu, Tunde Rahman, ya ce bai sanda wani gayyata daga Buhari ba.

KU KARANTA: Daga karshe, an bude babban filin jirgin saman Abuja

Yace: “Ba zaka iya taka hakkin mutane ba; ba zaka iya hana wani takara ba kamar yadda kundin tsarin mulki.”

“Yanzu ya ragewa mambobin jam’iyyar su zabi dan takararsu ta zaben fiddan gwanin kato bayan kato.”

“Dukkan yan takaran guda uku zasuyi takara a zaben fitar da gwanin. Tun da su uku sun dauki Fam, jam’iyyar za ta zaba wanda take so.”

Wasu majiya masu inganci ya nuna cewa babban dalilin da yasa Tinubu ke son ladabta Ambode shine wasu abubuwa da ya canza a shugabancin Legas da suka batawa Tinubu rai.

Tinubu ya bayyana niyyar maye gurbin Ambode da kwamishana Sanwoolu a zaben 2019. Shi kuma Ambode ya lashi takobin ba zai mika kai ba.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel