Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya nada sabon shugaban DSS yan makonni bayan dakatar da Daura

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya nada sabon shugaban DSS yan makonni bayan dakatar da Daura

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a ranar Alhamis, 13 ga watan Satumba, ya bayyana Yusuf Magaji Bichi a matsayin sabon darakta-janar na hukumar yan sandan farin kaya (DSS).

Sabon shugaban zai karbi aiki daga hannun Matthew Seiyeifa, wanda yam aye gurbin Lawal Daura da aka dakatar.

Garba Shehu, kakakin shugaban kasa ne ya bayar da sanarwar a wani jawabi da ya saki a yau.

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya nada sabon shugaban DSS yan makonni bayan dakatar da Daura

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya nada sabon shugaban DSS yan makonni bayan dakatar da Daura
Source: Depositphotos

Sabon shugaban zai fara aiki ne daga ranar Juma’a, 14 ga watan Satumba.

Mista Bichi yayi aiki a matsayin daraktan tsaro na jiha a jihohin, Jigawa, Niger, Sokoto da Abia.

KU KARANTA KUMA: Tarihi: Birgediya Zakariya Maimalari, kwararren jami’in soja na farko a Najeriya

Ya kuma rike matsayin darakta lokuta da dama, hadimin majalisar dokoki, darakta a hedkwatar tsaro da dai mukamai da dama.

Bichi na da mata da yara.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel