2019: PDP ta shiga zawarcin gwamnan APC da takarar sa ke rawa

2019: PDP ta shiga zawarcin gwamnan APC da takarar sa ke rawa

Jam’iyyar PDP a jihar Legas ta ce zata yi maraba da gwamna Ambode idan ya shirya fita daga jam’iyyar APC.

Sakataren yada labarai na jam’iyyar PDP a jihar Legas, Mista Taofik Gani, ya yi wannan kalami yayin wata tattaunawa da kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN).

Gani na wannan kalamai ne bayan samun rahotannin cewar tsohon gwamnan jihar Legas, Bola Tinubu, ya tsayar da kwamishinsa, Mista Jide Sanwo-Olu, domin ya fafata da gwamna Ambode a zaben fitar dad an takara na cikin gida.

"Duk wata jam'iyyar siyasa ba zata ki son ganin babban abokin hamayyar ta ya dawo cikinta ba. Muna maraba da Ambode idan har zai dawo jam'iyyar mu ta PDP," a kalaman Gani.

Sannan ya cigaba da cewa, "zamu yi farinciki da dawowar sa domin hakan zai kara mana damar lashe zaben 2019 a jihar Legas."

A satin da ya gabata ne kafafen yada labarai suka wallafa rahoton cewar gwamnan jihar Legas, Akinwunmi Ambode, na duba yiwuwar ficewarsa daga APC saboda sabanin da ya shiga tsakaninsa da jagoran jam’iyyar na kasa kuma tsohon gwamnan jihar Legas, Bola Tinubu.

2019: PDP ta shiga zawarcin gwamnan APC da takarar sa ke rawa

Ambode
Source: Depositphotos

Tsohon gwamnan na jihar Legas ya juyawa gwamna Ambode baya ne saboda canja wasu dokoki da ya yi bayan ya hau mulki a 2015, kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta rawaito.

Rashin jituwar dake tsakanin Tinubu da Ambode ta kara fitowa fili ne bayan wasu jiga-jigan ‘yan APC a jihar Legas da suka hada da mataimakin jam’iyyar APC na Legas, Cardinal James Odumbaku, da tsohon kwamishinan noma, Kaoli Olusanya, sun umarci Ambode ya mayar da fam din takarar da ya saya ko kuma a tsige shi daga kujerar gwamna.

DUBA WANNAN: Sojojin Najeriya sun yiwa 'yan Boko Haram da suka kai masu hari kisan kiyashi

Odumbaku da Olusanya sun fadawa Ambode hakan ne ranar Litinin da daddare a wurin taron da suka yi a Otal din Watercress dake Ikeja.

Rahotanni sun bayyana cewar yayin taron, dukkan shugabannin kananan hukumomin jihar Legas 20 da na hukumomin raya jihar 37 (LCDAS), sun saka hannun goyon bayan dan takarar da Tinubu ke so, Mista Babajide Sanwo-Olu.

Jagorororin jam’iyyar APC a jihar Legas sun ce ba zasu goyi duk dan takarar da bashi da goyon bayan tsohon gwamna Tinubu ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel