Shirin N-Power ya samar da abin yi ga Matasa 500, 000 a Najeriya - Osinbajo

Shirin N-Power ya samar da abin yi ga Matasa 500, 000 a Najeriya - Osinbajo

Akwai dubunnan matasa dake ci gaba da darawa gami da wadaka cikin yalwar arziki daidai gwargwado a sakamakon ribatar shirin nan na N-Power da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta dabbaka a kasar nan ta Najeriya.

A yayin da mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, shine umul aba isin tabbatar da wannan shiri a kasar nan, ya kuma bayyana cewa a halin yanzu akwai matasa 500, 000 dake ribatarsa ta fannonin aikace-aikace daban-daban.

Kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito, Mataimakin shugaban kasar ya bayyana cewa, adadin Matasa 500, 000 ne ke yakar bakin talauci da zaman banza irin na kashe wando ta hanyar wannan shiri da ya zamto tabarraki ga al'umma gami da bunkasa ci gaban kasar nan.

Osinbajo ya bayyana hakan ne yayin wani taro da majalisar dinkin duniya ta dauki nauyin gudanarwa cikin babban birnin kasar nan na tarayya a ranar Alhamis din da ta gabata.

Shirin N-Power ya samar da abin yi ga Matasa 500, 000 a Najeriya - Osinbajo

Shirin N-Power ya samar da abin yi ga Matasa 500, 000 a Najeriya - Osinbajo
Source: Depositphotos

A yayin taron mai taken muhimmancin shugabanni na addinai, Mataimakin shugaban kasar ya bayyana cewa, gwamnatinsu bisa jagoranci na shugaba Buhari ta kawo wasu sabbin shirye-shirye ma su tallafawa Mata da Matasa wajen rage rashin abin yi da kuma yakar katutu na bakin talauci.

KARANTA KUMA: Ba na shakkar yin fito-na-fito da Kwankwaso - Shekarau

Kazalika, mataimakin shugaban kasar ya bayyana cewa, shirye-shiryen na gwamnatinsu sun kuma kawo wani sabon tsari na ciyarwa a makarantu da a halin yanzu kimanin yara miliyan 9.2 ke amfana a cikin jihohi 26 na kasar nan.

Dangane da tabbatar da ci gaba da kwarar romon dimokuradiyya, Osinbajo ya bayyana cewa gwamnatinsu ta kuma dukufa wajen habaka tattalin arziki da adadin al'ummar kasar nan za su dogara a kai.

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, gwamnan jihar Benuwe, Samuel Ortom, ya bayyana cewa rayukan mutane 560 sun salwanta cikin watannin 9 kacal a jihar sa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Legit

Mailfire view pixel