Jalal Falal ya fasa shiga takarar Gwamnan Kaduna a karkashin APC

Jalal Falal ya fasa shiga takarar Gwamnan Kaduna a karkashin APC

Mun samu labari cewa Alhaji Jalal Falal wanda yana cikin masu neman Gwamnan Kaduna ya fasa shiga takarar Gwamnan da za ayi a Jam'iyyar APC. Falal yace ba a shirya gaskiya ba a zaben.

Jalal Falal ya fasa shiga takarar Gwamnan Kaduna a karkashin APC

Mai neman takara da Gwamna El-Rufai a APC ya hakura
Source: Depositphotos

Jalal Falal wanda kusan shi kadai ne ke neman yayi takara da Nasir El-Rufai a cikin Jam'iyyar APC mai mulki ya nuna cewa shi da mutanen sa sun zare hannun sa daga zaben 2019 bayan Jam'iyyar ta kama hanyar rashin adalci.

Falal ta bayyanawa manema labarai a makon nan cewa ba za su yi na'am da APC ta dauka a Kaduna na kin yi amfani da zaben kato-bayan-kato ba. Falal yace sun yi kokarin jawo hankalin uwar Jam'iyya amma abin ya ci tura.

KU KARANTA: Ban tsoron ja da Kwankwaso a Kano - Shekarau

'Dan siyasar ya bayyana cewa ba zai yi takarar fitar da gwani a Jam'iyyar APC ba domin kuwa matsayar da Jam'iyyar ta dauka ba mai bullewa bane. Falal Jalal yace an shirya kintsa rashin gaskiya wajen tsaida 'Yan takarar APC.

Matashin ‘Dan siyasar ya bayyana cewa duk da hakan ba zai fice daga Jam’iyyar APC ba domin kuwa shi ya kawo kan sa inda yace ko ba dade ko ba jima sai yayi Gwamna a Kaduna. Jalal ya godewa kokarin da Matasan Jihar su kayi masa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel