Kungiyar NLC ta ki amincewa da Mimiko a matsayin dan takaran shugaban kasa

Kungiyar NLC ta ki amincewa da Mimiko a matsayin dan takaran shugaban kasa

Kungiyar kwadago ta kasa (NLC) tayi watsi da shirin tsohon shugaban jam’iyyar Labour Party, Abdulkadir Abdulsalam na son tsayar da Olusegun Mimiko a matsayin dan takaran shugaban kasarta a zabe mai zuwa.

Mista Ayuba Wabba, shugaban NLC da Misis Ebere Ifendu, sakatariyar jam’iyyar Labour Party na kasa ta bayyana hakan a wani taron manema labarai a ranar Alhamis, 13 ga watan Satumba a Abuja.

A cewar Wabba, hakan na da matukar muhimmanci ga kungiyar kwadago ta bayyana zuciyarta akan zaben 2019.

Jam’iyyar Labour Party ta ki amincewa da Mimiko a matsayin dan takaran shugaban kasarta

Jam’iyyar Labour Party ta ki amincewa da Mimiko a matsayin dan takaran shugaban kasarta
Source: Depositphotos

Sunce babu yadda za’ayi Mimiko yayi takara a karkashin jam’iyyar Labour Party, cewa kungiyar kwadago da na kasuwanci suka yi rijistar jam’iyyar.

KU KARANTA KUMA: Yan takaran kujerar kujeran shugaban kasa a PDP sun shirya nemawa kansu mafita kafin zaben fidda gwani

Ya kara da cewa jam’iyyar Labour Party ba wuri bane da kowani irin dan takara zai shiga idan abubuwa suka daidaita sannan ya yasar da ita idan ya gama cin moriyar ganga.

Hakazalika, Misis Ebere Ifendu, babbar sakatariyar jam’iyyar tayi gargadi yan Najeriya day an takaran siyasa da su yi watsi da taron jam’iyyar da aka shirya yi a ranar 13 ga watan Satumba a Abuja.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel