Gwamnatin Kaduna zata mikawa 'yan kasar China kamfanunuwan da suka durkushe

Gwamnatin Kaduna zata mikawa 'yan kasar China kamfanunuwan da suka durkushe

- Kamfanonin kasar nan duk sun durkushe saboda babu jari, babu kuma kudin jari

- Gwamnatin Kaduna ta kira 'yan China suzo su farfado da kamfunnan

- Rashin wuta, kwararru shi ya hana kamfanoni ci gaba da habaka

Gwamnatin Kaduna zata mikawa 'yan kasar China kamfanunuwan da suka durkushe

Gwamnatin Kaduna zata mikawa 'yan kasar China kamfanunuwan da suka durkushe
Source: Facebook

Tawagar 'yan China da suka kawo ziyara jihar Kaduna don ganin inda zasu zuba jari, ta sami tarbar gwamnan Kaduna, malam, Nasir Ahmad Elrufai, a fadar gwamnatinsa, inda yayi kira da su zo su duba yadda zasu iya farfado da masana'antun da suka durkushe a jihar.

Masana'antun, wadanda sun hada na atamfofi da shadda, wadanda jihar tayi suna dasu a da, zamanin Ahmadu Bello Sardaunan Sokkoto, wanda ya kafa masana'antun don moriyar na baya.

DUBA WANNAN: An kai samame gidan su Leah Sharibu

Mrs Shuying Waang, shugabar tawagar, tace zasu duba yiwuwar farfado da kamfunnan, sannan zasu so su gyara harkar noma da samar da habaka samar da auduga domin sana'ar ta juya kowa ya mora, kasar nan da tasu ta China.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel