2019: Kashedin shugaba Muhammadu Buhari ga 'yan jam'iyyarsa ta APC

2019: Kashedin shugaba Muhammadu Buhari ga 'yan jam'iyyarsa ta APC

- Shugaban yayi godiya ga 'yan Najeriya da suka hada kudi suka saya masa fom din takara

- Yayi kira ga 'yan jam'iyyar da kada su saki jiki kan wai su suke mulki

- A yayin da ake sauyin jam'iyya, ana raba wa APC hankali

2019: Kashedin shugaba Muhammadu Buhari ga 'yan jam'iyyarsa ta APC

2019: Kashedin shugaba Muhammadu Buhari ga 'yan jam'iyyarsa ta APC
Source: Facebook

A lokacin da yaje mayar da om dinsa na takarar shugabancin kasar nan a zagaye na biyu, a jam'iyyarsa mai mulki ta APC, shugaba Buhari ya yi kashedi ga 'yan jam'iyyar da kada su kuskura su saki jiki su dauka sunfi karfin 'yan hamayya.

Ya kuma kuma kira 'yan Najeriya da su kula kada 'mugaye' su dawo musu mulki, wanda yake nufi da 'yan PDP.

Kasa da watanni biyar dai suka rage a fara zabukan kasa baki daya, kuma ana ta yayin sauyin sheka, zuwa cikin jam'iyya mai mulki, wasu kuma na ciki suna ficewa.

DUBA WANNAN: Harin Boko Haram a Damasak, Yadda batun yake

A yanzu kam, shugaban yayi godiya ga kungiyoyin da suka hada kudi suka saya masa fom, ya kuma kira sauran 'yan jam'iyya dasu zage damtse har sai sun kawo kujerunsu a babban zabe.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel