An salwantar da rayukan Mutane 560 cikin watanni 9 a jihar Benuwe - Ortom

An salwantar da rayukan Mutane 560 cikin watanni 9 a jihar Benuwe - Ortom

Tun ba yanzu ba sanin kowa ne cewa rikici ya tsananta a sassa daban-daban dake fadin kasar nan musamman mafi shaharar aukuwarsu a yankunan Arewa ta Gabas da kuma Arewa ta Tsakiya inda rikicin makiyaya da manoma ya yi kamari.

Kamar yadda shafin jaridar The Nation ya ruwaito, jihar Benuwe da ta kasance daya daga cikin jihohi dake yankin Arewa ta Tsakiya a kasar nan, rikita-rikitar makiyaya da manoma ta yi kamarin gaske inda ta salwantar da rayukan mutane bila adadin.

Mun samu rahoton cewa, rikicin makiyaya da manoma ya salwantar da rayukan mutane 560 cikin watanni 9 kacal a jihar Benuwe yayin da ya yi sanadiyar jefa dubunnan mutane neman mafaka a sansanan gudun hijira dake yankin Arewa ta Tsakiya.

Gwamnan jihar Benuwe, Samuel Ortom, shine ya bayyana hakan da cewar aukuwar hare-haren makiyayan ta hana tsugunno na fiye da rabin al'ummomi a muhallansu musamman wadanda ke kananan hukumomin Gwer ta Yamma, Makurdi, Guma, Logo da kuma Kwande.

Gwamnan jihar Benuwe; Samuel Ortom

Gwamnan jihar Benuwe; Samuel Ortom
Source: Depositphotos

Gwamnan ya kuma bayyana yadda wannan lamari na rashin tsaro, annoba gami da karancin kudi ya kalubalanci jagorancin sa musamman daga watan Janairun na wannan shekara ta 2018 kawowa yanzu.

Legit.ng ta fahimci cewa, gwamnan ya yi wannan furuci ne a muhallin tsohon shugaban majalisar dattawa, Dakta Iyorchia Ayu, yayin ganawa da manyan masu ruwa da tsaki na jam'iyyar sa ta PDP na kananan hukumomin Tarka, Buruku da kuma Gboko.

KARANTA KUMA: Tsohon gwamnan jihar Ondo, Mimiko, ya bayyana kudirin tsayawa takarar Kujerar Shugaban Kasa

Gwamna Ortom ya ci gaba da cewa, duk da wannan kalubale da gwamnatin sa ta fuskanta, ta taka muhimmiyar rawa ta gani musamman a bangaren kiwon lafiya, noma, ilimi da kuma raya karakara da ya sha alwashin kara hobbasa da kokori akan hakan muddin suka sake kada ma su kuri'u a babban zabe na 2019.

Ya kara da cewa, aukuwar hare-hare a jihar ta zarce ta makiyaya da manoma kadai, inda ya ce maharan sun hada gwiwa ne da wasu shugabanni na jihar da suka kudirci tsige sa daga kan kujerar sa ta gwamnatin jihar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel