Gwamna Masari ya yiwa Buhari alkawarin kuri'u Miliyan 2.5 daga jihar Katsina

Gwamna Masari ya yiwa Buhari alkawarin kuri'u Miliyan 2.5 daga jihar Katsina

Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina ya bugi kirji da cewar tuni kuri'u sama da miliyan 2.5 na jiran shugaban kasa Muhammadu Buhari daga al'ummar jihar idan har aka zo zaben shekara ta 2019.

Gwamna Masari ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ke amsa tambayoyi daga manema labarai a ranar Alhamis jim kadan bayan ganawar sirri da ya yi da shugaban kasa Buhari a cikin fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Ya ce al'ummar jihar Katsina na goyon bayan shugaba Buhari dari bisa dari, jihar ta ke mahaifa ga shugaban kasar.

KARANTA WANNAN: Buhari ya bukaci yan Nigeria su zabi APC don gujewa kuskuren 1999 zuwa 2015

A cewar sa: "Al'umar jihar Katsina na goyon bayan Buhari dari bisa dari kuma za su ci gaba da bashi goyon baya don samun nasara a zaben 2019."

Gwamna Masari ya yiwa Buhari alkawarin kuri'u Miliyan 2.5 daga jihar Katsina

Gwamna Masari ya yiwa Buhari alkawarin kuri'u Miliyan 2.5 daga jihar Katsina
Source: Facebook

Masari ya ce: "Bisa alkaluman da muke gani na mutanen da suka yi rijistar katin zabe a jihar, kaso 70 zuwa 80 za su zabi shugaban kasa Buhari ba tare da wani sabon tunani ba idan zabe ya zo.

"Duk da cewa bamu da cikakken masaniya kan adadin mutanen da suka yi rijistar katin zaben, kasancewar ba a kammala rijistar ba, ba wai kuma muna magana akan wadanda suka yi rijistar zaben 2015 ba, zaben da shugaban kasar ya samu kuri'u sama da Miliyan 1.5 daga jihar.

"Muna sa ran cewa zamu bashi karin kuri'u miliyan daya a zaben 2019 don ganin ya samu sama da kuri'u miliyan 2.5" a cewar gwamnan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel