Gwamna Ambode ya karyata rade-radin rikicin sa da Tinubu

Gwamna Ambode ya karyata rade-radin rikicin sa da Tinubu

Gwaman Jihar Legas Akinwumi Ambode ya karyata rade-radin cewa akwai kwantacciyar rigima tsakanin sa da Mai gidan sa Asiwaju Bola Tinubu. Tinubu ne dai yayi sanadin zaman Ambode Gwamna.

Gwamna Ambode ya karyata rade-radin rikicin sa da Tinubu

Ambode yace babu komai tsakanin sa da Tinubu sai alheri
Source: UGC

Kawo yanzu ana ta yada cewa Akinwumi Ambode yana rigima da tsohon Gwamnan Legas Bola Tinubu wanda Gwamnan yayi maza ya karyata inda yace maganar cewa Tinubu na neman hana sa tazarce a APC a 2019 ba gaskiya ba ne.

Gwamnan na Legas yayi wannan jawabi ne lokacin da ya gana da manyan Jam'iyyar APC a Garin Epe. Ambode yace sam babu wani rikici tsakanin sa da babban Jigon na Jam'iyyar APC mai mulki kamar yadda wasu ke rayawa.

KU KARANTA: An rasa wanda zai ja da Shugaban kasa Buhari a APC

Akinwumi Ambode ya nemi manyan APC na Legas su cigaba addua a wannan a lokaci inda ya kuma gode masu wajen ba sa goyon baya. Gwamnan yace babu Jam'iyyar da za ta doke APC a Legas da ma Najeriya gaba daya a zaben 2015.

Jam'iyyar APC a Legas ta zabi wadanda za su kada mata kuri'a wajen zaben fitar da gwani na kujerar Shugaban kasa da za ayi. Kawo yanzu dai mun ji cewa har fadar Shugaban kasa ta shiga tsakanin Tinubu da Gwamnan na Jihar Legas.

Jiya kun ji cewa Bola Tinubu wanda jigo ne a siyasar Yarbawa da kuma mutanen sa na yunkurin kakaba Mista Jide Sanwo-Olu a matsayin 'Dan takarar Gwamna a karkashin Jam’iyyar APC a zaben 2019.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel