Kotu ta yi watsi da karar da aka shigar kan a hana tilasta wa majalisa ta dawo zama kafin ranar 25 ga Satumba

Kotu ta yi watsi da karar da aka shigar kan a hana tilasta wa majalisa ta dawo zama kafin ranar 25 ga Satumba

Wata babbar kotu dake Abuja ta yi watsi da karar da aka shigar gabantakan a hana tursasa majalisa ta dawo zama kafin ranar 25 ga watan Satumba.

Sanata Isah Misau da Sanata Rafiu Adebayo dake biyayya ga Shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, ne suka shigar da karar.

Sun bukaci kotu da ta dakatar da yunkurin da ake yi na son tilasta wa sanatoci su dawo daga hutun da suke a yanzu.

Kotu ta yi watsi da karar da aka shigar kan a hana tilasta wa majalisa ta dawo zama kafin ranar 25 ga Satumba

Kotu ta yi watsi da karar da aka shigar kan a hana tilasta wa majalisa ta dawo zama kafin ranar 25 ga Satumba
Source: Depositphotos

Alkalin ya bayyana cewa wannan kara da aka shigar ba ta da ma’ana wadda a dalilin haka ya yi watsi da karar.

KU KARANTA KUMA: Buhari bai samu abokin adawa ba, zai fuskanci zaben fidda gwani na APC a Oktoba don tabbatar da shi

Shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki, David Mark, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da Sanata Jonah Jang, Gwamna Tambuwal da Ibrahim Dankwambo duk suna neman tikitin jam’iyyar PDP.

Amma dukkaninsu sun nemi takara ne ta hanyar da zai basu damar dawowa majalisar dattawa idan basu cimma kudirinsu na tsayawa takarar shugaban kasa ba.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel