Yadda batun yake: Wai Boko Haram ta shiga Damasak?

Yadda batun yake: Wai Boko Haram ta shiga Damasak?

- Sojojin sun kori yan ta'addan da suka kai hari Damasak

- Wasu yan garin sunce karar harsashi kawai sukaji

- Sojojin Najeriya sun halaka yan ta'addan da yawa

Yadda batun yake: Wai Boko Haram ta shiga Damasak?

Yadda batun yake: Wai Boko Haram ta shiga Damasak?
Source: Depositphotos

Sabani da rahoton da muka samu da farko, cewa yan ta'adda sun karbe garin Damasak dake Borno, majiya mai karfi tace tabbatar mana cewa rundunar sojojin Najeriya sun fatattaki yan ta'addan.

Majiyoyi da dama daga garin sunce karar harsashi kadai sukaji gurin karfe 6 na yamma, amma yan ta'addan basu shigo garin ba.

DUBA WANNAN: An raunata jama'a da yawa a harin Parisa

Hukumar Sojin Najeriya tace runduna ta 145 na garin Damasak domin fatattakar yan ta'addan da suka shiga garin gurin karfe 6 na yamma a ranar laraba.

"Matsananciyar gwagwarmaya ke faruwa yanzu tsakanin rundunar sojoji da yan ta'adda " inji mai magana da yawun hukumar Sojin Najeriya", inji Texas Chukwu.

Wata majiyar mu tace rundunar tayi nasarar halaka da yawa daga cikin yan ta'addan.

Wani mazaunin garin yace sun dai ji karar harsasai amma babu Dan ta'addan da ya shigo garin. Har sallar magriba sukayi a masallatai kafin su koma gidajen su.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel