An kai samame gidan su Leah Sharibu, inji mahaifinta

An kai samame gidan su Leah Sharibu, inji mahaifinta

- Yan fashi sun shiga gidansu Leah Sharibu

- Yan fashi sun kwashe mana dukiyoyi

- Sun hada da kayayyakin abincin mu da karamin jannareto

An kai samame gidan su Leah Sharibu, inji mahaifinta

An kai samame gidan su Leah Sharibu, inji mahaifinta
Source: Depositphotos

Wasu da ake zargin yan fashi ne sun afka gidansu Leah Sharibu, daya daga cikin yan makarantar da yan Boko Haram suka sace a watan Fabrairu a jihar Yobe.

An sace ta ne tare da yan makarantar su, amma sai aka saki sauran yaran bayan gwamnati ta agaza. Ita kuwa suka riqe ta bayan da taki barin addinin ta na kiristanci.

Babanta, Sharibu Nathan, ya sanar da majiyar mu a gidan shi dake Dapchi, jihar Yobe, Cewa yan fashi sun afka gidan shi. Amma yace ba babban hari bane.

"Tabbas yan fashi da makami sun afko gidanmu a ranar litinin, inda suka karbe mana kayan abinci da karamin janareton mu. Amma basu raunata kowa ba a yayin harin, " inji shi.

DUBA WANNAN: Afirka bata shirya aiki da 5G ba

Rahoton farko yace Matar Sharibu bata gidan lokacin da yan fashin suka afka musu. Tayi kururuwa ne bayan da ta dawo, ta tarar an kwashe kayayyakin ta.

Mista Sharibu yace wannan rashin ba komai bane Idan aka danganta shi da sace diyar su da akayi kwanaki.

Amma yace gidansu kawai akayi wa fashin a anguwar.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel