An ce sojoji su daina sanya inifom na aikinsu in sun shiga jama'a

An ce sojoji su daina sanya inifom na aikinsu in sun shiga jama'a

- Yakamata sojoji su dena yawo da khaki Idan basa cikin bariki

- Sukan rufawa yan ta'adda asiri Idan suna sanye da khaki

- Kar kotu ta yanke hukuncin da zai kawo barazana ga tsaron kasa

An ce sojoji su daina sanya inifom na aikinsu in sun shiga jama'a

An ce sojoji su daina sanya inifom na aikinsu in sun shiga jama'a
Source: Facebook

Wani Babban Lauya, Mista Femi Falana, ya shawarci gwamnatin tarayya da ta hana sojoji yawo da Khaki a wajen bariki domin kawo karshen wasu aiyukan ta'addanci a kasar nan.

Kamar yanda yace, wasu sojoji sanye da khaki kan rufawa yan ta'adda asiri har su ka ga cimma munanan burikan su.

Ya bada misali da wannan shahararren mai garkuwa da mutanen, Chukwudumeme Onwuamadike, alias Evans, wanda soja ke taimakon shi.

"Dole ne a bar saka khakin sojoji a cikin gari. Wannan yaron, Evans, soja ke biye dashi a duk lokacin da yayi garkuwa da mutum, wanda hakan ke sa sojojin tsaro su kyale su har su wuce da wanda suka sacen. Bayan bincike ne aka kama sojan da Naira miliyan 96.5 a asusun bankin shi.

DUBA WANNAN: An binne Kofi Annan

Amma Idan aka hana sojoji yawo da khaki, za'a rage yawan ta'addancin dake faruwa a kasar," Falana yace.

Ya shawarci shugaban kasa Muhammadu Buhari da kada yayi saken da kotu zata yanke hukuncin da zai kawo barazana ga harkar tsaro.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel