Buhari ya bukaci yan Nigeria su zabi APC don gujewa kuskuren 1999 zuwa 2015

Buhari ya bukaci yan Nigeria su zabi APC don gujewa kuskuren 1999 zuwa 2015

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci yan Nigeria da su kauracewa zabar mutanen da suka handame dukiyar al'umma daga 1999 zuwa 2015 a zaben 2019

- An samu yar tata-burza a lokacin da shugaban jam'iyyar APC na kasa Adams Oshiomhole ya bukaci Buhari ya biya N100 don karbar katin shaidar zama dan jam'iyyar

- Oshiomhole ya kuma shaidawa shugaban kasa cewa zuwa yanzu jam'iyyar ta samu mambobi miliyan 15.6 daga sassa daban daban na kasar

A jiya ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci yan Nigeria da su kauracewa zabar mutanen da suka handame dukiyar al'umma daga 1999 zuwa 2015 a zaben 2019 da ke gabatowa.

An samu yar tata-burza a babban dakin taron majalisar zartaswa na jam'iyyar APC da ke cikin sakatariyar jam'iyyar na kasa, a Abuja, lokacin da shugaba Buhari ya je mayar da fam din tsayawa takar shugabancin kasar karkashin jam'iyyar ta APC.

An samu yar tata-burzar ne a lokacin da shugaban jam'iyyar APC na kasa Adams Oshiomhole ya bukaci shugaba Buhari da ya biya N100 don karbar katin shaidar zama dan jam'iyyar kamar yadda kowa ke biya.

KARANTA WANNAN: Amina Muhammad ta bayyana dalilin da yasa ake kiran ministar shara a Nigeria

Oshiomhole ya kuma shaidawa shugaban kasa cewa zuwa yanzu jam'iyyar ta samu mambobi miliyan 15.6 daga sassa daban daban na kasar.

Buhari ya bukaci yan Nigeria su zabi APC don gujewa kuskuren 1999 zuwa 2015

Buhari ya bukaci yan Nigeria su zabi APC don gujewa kuskuren 1999 zuwa 2015
Source: Depositphotos

Shugaban kasa Buhari, wanda ya bayyana godiyarsa ga wadanda suka yi hadaka wajen saya masa fam din tsayawa takara, ya shaidawa yan Nigeria cewa idan har aka sake bashi dama a zabe mai zuwa, zai ci gaba da shugabantar kasar iyakar iyawarsa.

Ya ce: "A yau ga shi ina tsaye a gabanku, tare da abokain aiki dana rayuwar yau da kullum don gabatar da kaina ga jam'iyyar, tare da mayar da fam din tsayawa takarar tazarce karkashin jam'iyyar APC a zaben 2019 mai zuwa.

"Ina rokon yayan wannan jam'iyya mai albarka da su zage damtse, su maida himma wajen shirye shirye don samun nasarar zaben 2019. Ya zamar mana wajibi mu kaucewa zabar wadanda suka murkushe wannan kasar daga 1999 zuwa 2015 don kar su dawo su sake mulkarmu" a cewar Buhari.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Tags:
Mailfire view pixel