Buhari bai samu abokin adawa ba, zai fuskanci zaben fidda gwani na APC a Oktoba don tabbatar da shi

Buhari bai samu abokin adawa ba, zai fuskanci zaben fidda gwani na APC a Oktoba don tabbatar da shi

- Shugaban Kasa Buhari bai samu abokin adawa ba a jam'iyyar APC akan kudirinsa na neman tazarce

- Sai dai zai fuskanci zaben fidda gwani da wakilan jam'iyyarsa zasu gabatar a watan Oktoba kamar yadda doka ta tanadar

- Daga nan ne za'a tabbatar da shi kai tsaye a matsayi wanda zai tsayawa jam'iyyar takara a zabe mai zuwa

Yayinda aka rufe shafin mayar da fam din neman takara a karkashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a ranar Laraba, 12 ga watan Satumba, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ne dan takara guda da ya yanki fam din takaran kujerar shugaban kasa.

Don haka ya zama baida abokin adawa a kudirinsa na yin tazarce a karkashin jam’iyyar mai mulki.

Sannan kuma zai taka sauran matakai da aka tanada kafin a sanar das hi a matsayin dan takaran shugaban kasa a jam’iyyar APC na zaben da za’a yi a shekara mai zuwa.

Buhari bai samu abokin adawa ba, zai fuskanci zaben fidda gwani na APC a Oktoba don tabbatar da shi

Buhari bai samu abokin adawa ba, zai fuskanci zaben fidda gwani na APC a Oktoba don tabbatar da shi
Source: Depositphotos

Bisa ga dokar zabe na 2010 kamar yadda aka gyara, duk dan takaran da baida abokin adawa zai fuskanci wani taro na mussaman daga jam’iyyarsa domin su tabbatar da tsawarsa a matsayin dan takaransu.

Abunda hakan ne nufi shine duk da cewar Buhari ne kadai ya mallaki tikitin APC, ya zama dole ya fuskanci tsarin tabbatar das hi ta hanyar zaben fidda gwani na wakilai kamar yadda hukumar zabe mai zaman kanta ta gindaya a wasu makonni da suka gabata.

A jiya Laraba, 12 ga watan Satumba ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mayar da fam dinsa na takara a sakatariyar APC dake Abuja.

KU KARANTA KUMA: Masarautar Kano na shirin fitar da doka akan yawaitar mutuwar aure

A baya Legit.ng ta rahoto cewa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta bayyana a ranar Alhamis, 13 ga watan Satumba cewa bata damu da sauya shekar kakakin majalisar wakilai Yakubu Dogara zuwa jam’iyyar Peoples Democratic Congress (PDP) ba.

A cewar jam’iyyar mai mulki, Dogara bai da kimar siyasa wadda zata kalla har tace tayi babban rashi, jaridar Premium Times ta ruwaito.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel