2019: Jam’iyyar APC ta yi min kora da hali - Dan takarar shugaban kasa

2019: Jam’iyyar APC ta yi min kora da hali - Dan takarar shugaban kasa

- Mista Adamu Garba II ya ce bai sayi fam din takarar shugaban kasa ba saboda shawarar da jam’iyyar APC ta yanke na sayar da fam din a kan miliyan N45m

- A jiya ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mayar da fam dinsa na takara da wata kungiya ta saya masa kyauta

- Dan takarar ya zargi jam’iyyar APC da kara farashin fam din takarar shugaban kasa da gan-gan domin yiwa ragowar ‘yan takarar kora da hali

Mai neman jam’iyyar APC ta tsayar da shi takarar shugaban kasa, Mista Adamu Garba, ya ce bai sayi fam din takarar shugaban kasa ba saboda zuga farashin fam din da shugabannin jam’iyyar suka yi.

Dan takarar ya bayyana cewar da gan-gan jam’iyyar ta APC ta kara farashin fam din takarar shugaban kasa domin yiwa ragowar masu son yin takara da shugaba Buhari kora da hali.

2019: Jam’iyyar APC ta yi min kora da hali - Dan takarar shugaban kasa

Adamu Garba
Source: Original

Mista Garba ya zargi shugabancin jam’iyyar da yin burus da kiraye-kirayen da aka yi na son su rage farashin fam din takarar shugaban kasa tare da bayyana cewar yin hakan yunkuri ne na tabbatar da cewar ragowar ‘yan takara basu samu dammar sayen fam din ba.

DUBA WANNAN: Sabon salo: PDP ta zo da sabon tsari a zaben fitar da dan takarar shugaban kasa

Dan takarar ya ce yana tuntubar magoya bayansa da abokan arziki domin daukan matakin da ya dace.

A jiya, Laraba, ne shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya mayar da fam dinsa na takara da wata kungiyar ‘yan kishin kasa suka saya masa kyauta.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel