Kotu ta sa a yiwa wani bulala saboda yada fitina a unguwarsu

Kotu ta sa a yiwa wani bulala saboda yada fitina a unguwarsu

Kotu ta bayar da umurnin a yiwa wani mutum bulala bayan an same shi yana sayar da wiwi a wata dandali da ke garin Kubuwa a babban birnin tarayya Abuja. Kotun tayi masa gargadi ya canja halayensa domin kasancewa dan kasa na gari.

A yau, Alhamis, wata kotu da ke zamanta a Kubwa ta bayar da umurnin yiwa wani Markus Joshu'a bulala 12 saboda samunsa da laifin tayar da hankulan jama'a.

Alkalin kotun, Abdulwahab Mohammed, ya gargadi Joshua ya gyra halayensa kana a guji aikata abinda zai jefa shi cikin matsala.

An yanke wa Joshua hukunci ne bayan kotu ta same shi da laifin tayar da hankalin jama'a.

Kotu ta umurci a yiwa wani mutum bulala saboda ya fitini jama'a

Kotu ta umurci a yiwa wani mutum bulala saboda ya fitini jama'a
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Babban malamin Islama na son a rage albashin 'yan siyasa

Mai shigar da kara, Babajide Olanipekun ya shaidawa kotu cewa an kama Joshua ne a wata dandali da ke kauyen Kubuwa a ranar 9 ga watan Satumba.

Ya ce Joshua yana busa hayaki kuma yana sayar da wani ganye da ake zargin wiwi ce.

"An gano kullin ganyen wiwi 40 a tare da Joshua bayan an gudanar da bincike," inji Olanipekun.

Laifin da Joshua ya aikata ya ci karo da sashi na 183 na Penal Code.

A wani rahoton, Legit.ng ta ruwaito cewa wasu gungun 'yan bindigan sun kai farmaki garin Badarawa da ke karamar hukumar Shinkafi ta jihar Zamfara a safiyar Alhamis.

'Yan bindigan sun kashe mutane 13 tare da raunatta wasu da dama.

Ba'a san dalilin da yasa 'yan bindigan suka kai harin ba amma tuni 'yan sanda da sojojin Najeriya sun hallara kauyen idan wasu ke sintiri a garin sannan wasu daga cikinsu suna bin sahun 'yan bindigan domin gano inda suke buya a daji.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel