Mu na da tabbatattun mambobi 15.6m masu rijista ta jam'iyyar APC - Oshiomhole

Mu na da tabbatattun mambobi 15.6m masu rijista ta jam'iyyar APC - Oshiomhole

Kamar yadda shafin jaridar Daily Trust ya ruwaito, a ranar Larabar da ta gabata ne shugaban jam'iyyar APC na kasa, Kwamared Adams Oshiomhole, ya bayyana adadin tabbatattun mambobi masu rajista ta jam'iyyar a fadin kasar nan.

Oshiomhole ya bayyana cewa, a halin yanzu jam'iyyar ta su ta APC na da tabbatattun mambobi miliyan 15.6 masu rajista dake da mallaki na katin shaida ta jam'iyyar.

Shugaban jam'iyyar ya bayyana hakan ne a shelkwatar jam'iyyar yayin da shugaban Kasa Muhammadu Buhari ke mayar da fam din sa na bayyana kudirin takarar kujerarsa a babban zabe na 2019.

Mu na da mambobi 15.6m masu rijista ta jam'iyyar APC - Oshimhole

Mu na da mambobi 15.6m masu rijista ta jam'iyyar APC - Oshimhole
Source: Depositphotos

Yayin jawabansa Kwamared Oshiomhole ya kuma bayyana cewa, jam'iyyar ta kudirci tabbatar da gaskiya da kuma adalci wajen gudanar da zaben fidda gwani a watan gobe.

A yayin haka ne shugaban jam'iyyar ya bayyana cewa, wannan adadi na mambobi da ta tantance za su tabbatar da gudanar zaben cikin inganci na gaskiya da amana.

KARANTA KUMA: Tsohon gwamnan jihar Ondo, Mimiko, ya bayyana kudirin tsayawa takarar Kujerar Shugaban Kasa

Rahotanni sun bayyana cewa, Kwamared Oshiomhole da shugaba Buhari na nan akan bakansu na kira kan gudanar da zabe na 'yar tinke sabanin yadda aka saba a baya na amfani da zababbun wakilan jam'iyya yayin zaben fidda gwani na jam'iyyu kasar nan.

Kazalika jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, an tsananta tsaro yayin da shugaba Buhari ya ziyarci shelkwatar jam'iyyar dake unguwar Wuse a babban birni na tarayya domin mayar da fam din sa na bayyana kudirin takara a ranar Larabar da ta gabata.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel