APC tayi magana akan sauya shekar da Dogara yayi zuwa PDP

APC tayi magana akan sauya shekar da Dogara yayi zuwa PDP

- Jam'iyyar APC ta nuna halin ko in kula da komawar Dogara PDP

- Tace ta dade da sanin cewa yana aiki tare da jam'iyyar adawar

- Kakakin majalisar wakilan Yakubu Dogara dai ya yanki tikitin sake takara amma dai a PDP

Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta bayyana a ranar Alhamis, 13 ga watan Satumba cewa bata damu da sauya shekar kakakin majalisar wakilai Yakubu Dogara zuwa jam’iyyar Peoples Democratic Congress (PDP) ba.

A cewar jam’iyyar mai mulki, Dogara bai da kimar siyasa wadda zata kalla har tace tayi babban rashi, jaridar Premium Times ta ruwaito.

APC tayi magana akan sauya shekar da Dogara yayi zuwa PDP

APC tayi magana akan sauya shekar da Dogara yayi zuwa PDP
Source: Depositphotos

“Mun karanta rahotannin cewa ya yanki fam din takara na PDP, hakan ba abun mamaki bane domin tuni muka san cewa yana aiki tare da jam’iyyar adawan,” inji kakakin jam’iyyar APC, Nabena.

A daren ranar Laraba, 12 ga watan Satumba ne muka samu labarin cewa kakakin majalisar wakilan ya yanki fam din sake takaran dan majalisar wakilai a karkashin jam’iyyar PDP.

KU KARANTA KUMA: Babu makawa APC ce zata kawo jihar Sokoto – Sanata Gada

Hakan na zuwa ne kwana daya bayan Dogara ya sanar da kudirinsa na sake takara amma yaki bayyana a wacce jam’iyyar zai yi takaran a lokacin wani gangami a Abuja wadda ya samu halarttan tarin magoya bayansa.

Wasu na ganin Dogara bai bi sigar da ya dace ba wajen sauya shekar nasa, domin kai tsaye ya yankin fam din jam’iyyar adawa ba tare da ya sanarwa tsohuwar jam’iyyarsa niysansa na barinta ba.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel