An umarci Gwamnatin Tarayya ta biya Jones Abiri Naira Miliyan 10.5

An umarci Gwamnatin Tarayya ta biya Jones Abiri Naira Miliyan 10.5

Dazu nan labari ya zo mana cewa Kotu ta ci Gwamnatin Shugaban kasa Muhamadu Buhari tarar kudi a dalilin rufe wani 'Dan jarida. Hukumar DSS ce ta rufe Jones Abiri na tsawon lokaci ta hana sa ganawa da Lauyoyi da Iyalin sa da Likitocin sa.

An umarci Gwamnatin Tarayya ta biya Jones Abiri Naira Miliyan 10.5

Hukumar DSS ta rufe Abiri ta hana sa ganawa da kowa
Source: Depositphotos

Wani Alkalin babban Kotun Tarayya da ke babban Birnin Abuja Nnamdi Dimgba ya umarci Gwamnatin Tarayya tayi maza ta biya wannan Bawan Alla Jones Abiri kudi har Miliyan 10.5 a dalilin garkame sa da aka yi wanda ya sabawa shari’a.

A yau Alhamis ne babban Alkali Nnamdi Dimgba ya yanke hukunci cewa Hukumar tsaro masu fararen kaya watau DSS ta biya ‘Dan jaridar nan da ta tsare na fiye da shekaru 2 watau Jones Abiri kudi har Naira Miliyan goma da rabi.

Tun a tsakiyar 2016 ne Jami’an DSS su kayi ram da Abiri inda aka zarge sa da kokarin taimakawa Tsagerun Neja-Delta wajen yada ta’addanci. A watan jiya ne Gwamnatin kasar ta saki Abiri bayan an rufe sa na tsawon watanni kusan 25.

KU KARANTA: Matar Sojan da ya bace ta fito tayi magana gaban Duniya

DSS ta fake ne da wata dokar kasa da ke hana ta’addanci wajen rufe Abiri. Sai dai ‘Dan jaridar da ke aiki a Jihar Bayelsa ya kai kara Kotu inda ya nemi a biya sa Naira Miliyan 200 na cin zarafin sa da keta masa hakki da aka yi a kasar.

Alkalin Kotun dai ya ba Lauyan ‘Dan Jaridar watau Femi Falana gaskiya inda ya bada hukunci cewa Jami’an tsaron sun wuce gona da iri har sun fita daga hurumin dokar ta hana ta’addanci. Dalilin haka ne aka ci Gwamnatin Tarayya tarar kudi.

DSS ta zargi ‘Dan jaridar da neman makudan kudi daga Kamfonin man Agip da kuma Shell. Shi dai ‘Dan Jaridar ya bayyana cewa bai san da wannan laifi da ake zargin sa da shi ba don haka ya tafi Kotu inda ya samu Lauyoyi su ka tsaya masa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel