Sanata Shehu Sani ya taya Buhari murnar mika fam din tazarce

Sanata Shehu Sani ya taya Buhari murnar mika fam din tazarce

Mun samu labari cewa fitaccen Sanatan nan na Jam’iyyar APC Shehu Sani ya taya Shugaban kasa Muhammadu Buhari murna bayan ya mika fam din sa na sake neman takara a karkashin APC.

Sanata Shehu Sani ya taya Buhari murnar mika fam din tazarce

Shehu Sani ya aikawa Buhari sakon murna bayan ya cike fam din takara
Source: UGC

Sanata Shehu Sani wanda ba bako bane wajen fitowa ayi magana a kafofin sadarwa na zamani yayi wa wasu daga cikin masu neman takara a zaben 2019 shagube inda ya nuna cewa wasun su sun saye fam biyu saboda gudun biyu babu.

Sanatan yayi wannan bayani ne a shafin sa na Tuwita a shekaran jiya inda ya bayyana cewa ya tuntubi wasu ‘Yan siyasa ‘Yan uwan sa da su ka yanki fam biyu dalilin hakan sai su ka fada masa cewa su na gudun ace sun tashi a tutar babu ne.

‘Dan Majalisar da ke wakiltar Jihar Kaduna ya taya Shugaba Buhari murna bayan ya mika fam din sa na neman zarcewa a kan mulki. Wasu Bayin Allah ne dai su ka hadawa Shugaban kasar kudi Miliyan 45 domin saya masa fam din na sa.

KU KARANTA: Shehu Sani ya caccaki wasu ‘Yan takarar Shugaban kasan 2019

A Ranar Talata ne Shugaba Muhammadu Buhari ya karbi fam din da aka saya masa na takarar Shugaban kasa. A jiya ne kuma Shugaban kasar ya mika fam din na sa a gaban manyan Jam’iyyar APC domin nuna shirin sa na takara a zaben 2019.

Shi ma dai Sanatan tuni ya saye fam din sa inda ya bayyana cewa wasu Matasa sun nemi su saye fam din tazarcen a madadin sa amma ya hana su. Kwanaki dai Sanata Shehu Sani ya gana da Shugaba Buhari a lokacin da yake hutun Sallah a Daura.

Kun san cewa Majalisar Dattawa Bukola Saraki da wasu manyan Sanatoci irin su David Mark, Jonah Jang, da Rabiu Kwankwaso za su iya yin biyu-babu a zabe mai zuwa bayan duk sun fito takarar kujerar Shugaban kasa a Jam’iyyar adawa ta PDP.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel