'Karin Albashi: 'Kungiyar 'kwadago ta bai wa Gwamnatin tarayya wa'adin kwanaki 14 ta kammala aikin ta

'Karin Albashi: 'Kungiyar 'kwadago ta bai wa Gwamnatin tarayya wa'adin kwanaki 14 ta kammala aikin ta

A ranar Larabar da ta gabata ne kungiyar kwadago ta Najeriya, ta bai wa gwamnatin tarayya wa'adin makonni biyu domin kwamitin da ta kafa kan karin albashin ma'aikata ya kammala aikinsa tare da gabatar da bincike domin cimma matsaya.

Kamar yadda shafin jaridar Daily Trust ya ruwaito, kungiyar ta bai wa gwamnatin tarayya wannan wa'adi domin ta kammala duk wani aiki na cimma matsaya tare da bayyana mafi karancin albashin ma'aikata a kasar nan.

Shugaba Buhari tare da Ministan 'Kwadago; Chris Ngige

Shugaba Buhari tare da Ministan 'Kwadago; Chris Ngige
Source: Depositphotos

A yayin wani taro da kungiyar ta gudanar can jihar Legas bisa jagorancin shugabanta, Bobboi Bala Kaigama, ta gargadi gwamnatin tarayya muddin ta wuce wannan kwanaki na wa'adi to kuwa ba bu shakka za ta fuskanci fushinta ta fuskar rashin samun kwanciyar hankali cikin harkokin kwadago a kasar nan.

KARANTA KUMA: Wani Matashi ya sheke 'Dan uwansa har Lahira kan N200 a jihar Legas

Legit.ng ta fahimci cewa, kungiyar ta huro wannan wuta ne a sakamakon furucin ministan kwadago, Dakta Chris Ngige, wanda kwanaki kadan da suka gabata ya bayyana cewa kwamitin na bukatar tsawaita lokaci domin kammala tuntube-tuntubensa da gwamnatin ta tarayya.

Kaigama wanda ya fusata kan furucin Minstan ya bayyana cewa, ba zai yiwu su ci gaba da zama na jiran tsammani ba tare da ma'aikatan kasar nan sun san makomar su ba.

A yayin haka jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari tare da tawagarsa za su shilla kasar Amurka cikin mako mai zuwa domin halartar wani babban taro na majalisar dinkin duniya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel