Na gwammace na mutu abubuwa su gyaru – Matashi ya hau kan falwayan kamfanin sadarwa saboda halin yunwan da yan Najeriya ke ciki

Na gwammace na mutu abubuwa su gyaru – Matashi ya hau kan falwayan kamfanin sadarwa saboda halin yunwan da yan Najeriya ke ciki

Wani matashi dan shekara 28 da haihuwa mai suna Nurudeen Iliyasu, yah au kan falwayan kamfanin sadarwa a birnin tarayya Abuja domin nuna bacin ransa kan yadda abubuwa suka tabarbare a kasan.

Legit.ng na kawo muku rahoton cewa an ga mutumin saman falwaya misalin karfe 12 na ranan Asabar a Unguwar AYA a Abuja.

Iliyasu yace ba zai sauka daga kan falwayan ba sai bayan kwanaki bakwai, kuma ya shirya sadaukar da rayuwarsa domin cigaban Najeriya.

KU KARANTA: Anyi musayar wuta tsakanin yan Boko Haram da Soji a Damasak

Yace: “Ina yajin aikin yunwa kuma kuncin da kasa ke ciki ya sani. Ba zan gushe a nan ba har tsawon kwanaki bakwai kuma ban ki in mutu a nan ba.”

“Idan mutuwa ne zai canza tattalin arzikin kasa, toh na shirya mutuwa domin wasu suyi rayuwa mai kyau.”

“Na dauki kwanaki yanzu cikin yunwa, hakazalika wasu yan Najeriya. Idan na mutu akan falwayan ne babu damuwa. Babu hanyoyi masu kyau a kasa sai dai cikin Abuja.”

‘Likitoci sunce mutum zai iya rayuwa ba tare da abinci ba muddin zai sha ruwa da wasu kwanaki, nayi imanin zan iya, kuma idan na gaza, zan mutu.”

Iliyasu ya jaddada cewa komai ya tabarbare a najeriya, harakar ilimi, kiwon lafiya, ayyukan jin dadin jama’a da sauran su.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel