Wani Matashi ya sheke 'Dan uwansa har Lahira kan N200 a jihar Legas

Wani Matashi ya sheke 'Dan uwansa har Lahira kan N200 a jihar Legas

Wani Matashi dan shekara 34, Moyowa Olabiyi, ya debo ruwan dafa kansa can jihar Legas yayin da a ranar Larabar da ta gabata ya gurfana gaban wata kotun majistire dake zamanta a unguwar Ebute Meta bisa laifi na kisan gilla kan kudi har N200.

Olabiyi ya gurfana gaban alkalin kotun, Mista O. O Olatunji, bisa laifi na kisan wani Matashi kan kudi N200, inda duk wani kokarinsa na rokon sassauci bai karbu ba yayin da kotun ta bayar da umarnin garkame shi har na tsawon kwanaki 30 a gidan kaso na Ikoyi kafin ta sake waiwayonsa.

Kamar yadda shafin jaridar Daily Trust ya ruwaito, Mista Olatunji ya mika wannan lamari na shari'a zuwa ga hukumar zartar da hukunce-hukunce ta jihar domin tuntuba da neman shawarwarin ta.

Jami'in dan sanda mai shigar da kara gaban kotun, Oladele Adebayo ya bayar da shaidar cewa, Olabiyi ya aikata wannan mummunan laifi ne da misalin karfe 6.30 na yammacin ranar 26 ga watan Agusta a wani gida mai lamba ta 23 dake unguwar Magodo a jihar ta Legas.

Wani Matashi ya sheke 'Dan uwansa har Lahira kan N200 a jihar Legas

Wani Matashi ya sheke 'Dan uwansa har Lahira kan N200 a jihar Legas
Source: Depositphotos

Adebayo ya ci gaba da cewa, wanda ake zargi tare da wasu mutane biyu masu hannun cikin wanna laifi da a halin yanzu sun yi aron kafar kare sun kar wani Matashi, Akeem Ajilogba, yayin da wani sabani ya shiga tsakanin su kan N200.

KARANTA KUMA: Najeriya ba ta taba shugaba wanda bai cancanci jagoranci ba tamkar Buhari - Atiku

Legit.ng ta fahimci cewa, Matasan uku sun aikata laifi na su da makami na Adda inda wannan lamari ke cin karo da sashe na 223 da kuma na 233 cikin dokokin jihar ta Legas da ba bu wani hukunci face na makamancin wanda suka aikata.

Kazalika, Alkalin kotun ya daga sauraron karar zuwa ranar 11 ga watan Oktoba domin ci gaba da shari'ar kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Legit

Mailfire view pixel