Tonon Silili: WAEC za ta bayyana sakamakon jarabawar wani dan takarar gwamna

Tonon Silili: WAEC za ta bayyana sakamakon jarabawar wani dan takarar gwamna

- Kotu ta baiwa hukumar gudanar da jarabawar WAEC umurnin fitar da sakamakon jarabawar Sanata Ademola Adeleke tare da yin rantsuwa akan sakamakon

- Kotun ta umurci WAEC ta da tabbatar da wannan sakamakon cikin kwanaki biyar

- Sanata Ademola Adeleke yana takarar gwamnan jihar Osun karkashin jam'iyyar PDP

Wata babbar kotun shari'a ta gwanmnatin tarayya da ke Abuja ta baiwa hukumar jarabawar WAEC umurni, ta hanyar babban darakta ko wani babban jami'i na hukumar, da ta fitar da sakamakon jarabawa, da zai tabbatar da cewa dan takarar gwamnan jihar Osun, karkashin jam'iyyar PDP, Sanata Ademola Adeleke ya zana jarabawa ko bai zaina ba.

Sanata Ademola Adeleke, wanda ya yi ikirarin zana jarabawar WAEC da lambar jarabawa 19645/149, a babbar makarantar sakandire ra Ede Muslim, da ke jihar Osun, a zangon jarabawa a Mayu/Yuni 1981.

Kotun ta umurci WAEC ta da tabbatar da wannan sakamakon cikin kwanaki biyar.

KARANTA WANNAN: APC ta karyata rahoton EIU/HSBC na cewar tattalin arziki zai karye idan Buhari ya zarce

Sanata Ademola Adeleke

Sanata Ademola Adeleke
Source: Facebook

Haka zalika kotun ta baiwa hukumar jarabawar WAEC umurnin gabatar da takardar rantsuwa na cewar dan takarar sanatan ya zana jarabawar WAEC a babbar makarantar sakandire ra Ede Muslim, da ke jihar Osun, a zangon jarabawa a Mayu/Yuni 1981.

Wannan umurni da kotu ta bayar ya biyo bayan wata kara da abokan karawar Sanatan suka shigar, Wahab Adekunle Raheem da Adam Omosalewa Habeeb, inda suka bukaci kotun ta umurci hukumar WAEC da ta bayyana sakamakon jarabawar Sanata Ademola Nuruddeen Adeleke da wasu mutane biyu.

Wadanda suke a matsayin masu kare wadanda ake karar sune jam'iyyar PDP da kuma hukumar gudanar da zabe ta kasa INEC

Those joined as defendants in the suit are the Peoples Democratic Party (PDP) and the Independent National Electoral Commission (INEC).

A karshe, kotun ta kuma umurci hukumar jarabawar WAEC da ta raba takardun sakamakon zana jarabawar da kuma takardar rantsuwa ga dukkanin masu karar da wadanda ake kara kafin nan da kwanaki biyar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel