Shugaba Buhari ya cika burin talakawan Najeriya - Onochie

Shugaba Buhari ya cika burin talakawan Najeriya - Onochie

- Hadimar Shugaban Kasa tace Buhari ya cika wa talakawan Najeriya burinsu

- A ranar Laraba, 12 ga watan Satumba ne shugaban kasar ya mayar da fam dinsa na takara

- Shugaba Buhari ya bukaci yan Najeriya da kada su bari PDP ta dawo mulki

Bayan mayar da fam din takara da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yayi a sakatariyar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) dake Abuja a ranar Laraba, 12 ga watan Satumba, Misis Lauretta Onochie hadimarsa ta bayyana cewa shugaban kasar ya cika burin talakawan Najeriya.

Lauretta Onochie ta rubuta a shafinta na twitter cewa: “A yau mun shaida lokacin da Shugaban kasa @MBuhari ke cika burin talakawan Najeriya wadanda ke samun ingantaccen rayuwa a karkshinsa.

Shugaba Buhari ya cika burin talakawan Najeriya - Onochie

Shugaba Buhari ya cika burin talakawan Najeriya - Onochie
Source: Depositphotos

“Ya mayar da cikakken fam dinsa na takaran kujerar shugabancin kasa a karkashin jam’iyyar APC. Kuma shugaban APC da kwamitin masu ruwa da tsaki sun amshi fam."

Yayinda yake mayar da fam din Shugaba Buhari ya bayyana cewa ya zama dole ayi kokari don ganin ba’a bari wadanda suka tabarbara kasar daga 1999 zuwa 2015 basu dawo mulki ba.

Ya nuna godiya ga kungiyar siyasar da suka siya masa fam din naira miliyan 45.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa hukumar zabe mai zaman kan ta ta kasa watau Independent National Electoral Commission (INEC) a turance ta karin haske game da batun yiwuwar daga zabukan gama gari na shekarar 2019 da take shirin gudanarwa a shekarar 2019.

KU KARANTA KUMA: Yanzu-yanzu: Jirgin Ali Modu Sheriff ta sabbaba kulle filin jirgin saman Abuja

Kamar dai yadda muka samu, a cikin wata sanarwar da jami'in hulda da jama'a na hukumar, Mista Rotimi Oyekanmi ya sa wa hannu ya kuma rabawa manema labarai yace hukumar bata da wani kuduri na zahiri ko na boye na daga zaben mai zuwa.

Legit.ng ta samu cewa a cikin sanarwar, Mista Rotimi Oyekanmi ya kara da cewa wannan karin hasken ya zama dole ga hukumar musamman ma ganin yadda wasu jaridu suka buga labarin cewa wai shugaban hukumar yace za'a iya dage zaben.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel