Zaben 2019: Yan kasuwan jihar Kaduna sun kunyanta Gwamna El-rufai

Zaben 2019: Yan kasuwan jihar Kaduna sun kunyanta Gwamna El-rufai

- Yan kasuwan jihar Kaduna sun kunyanta Gwamna El-rufai

- Kungiyoyin yan kasuwa sun ce babu su a cikin masu siya masa fom

Mambobin kungiyar 'yan kasuwar jihar Kaduna da suka hada da masu hada-hadar man fetur na Independent Petroleum Marketers Association of Nigeria (IPMAN) a turance sun yi magana game da batun siyawa Gwamnan jihar Kaduna Nasiru El-rufa'i fom din takarar tazarce a zaben 2019.

Zaben 2019: Yan kasuwan jihar Kaduna sun kunyanta Gwamna El-rufai

Zaben 2019: Yan kasuwan jihar Kaduna sun kunyanta Gwamna El-rufai
Source: Depositphotos

KU KARANTA: INEC tayi karin haske game da yiwuwar kara daga zaben 2019

Kungiyar dai ta IPMAN, kamar yadda muka samu, ta nesanta kan su da labarin da ke yawo na cewa wasu 'yan kasuwar jihar sun hada kudi sun siyawa Gwamna El-rufai fom din takarar tazarce a zaben.

Legit.ng ta samu haka zalika cewa suma wasu 'yan kungiyar masu tireda ta jihar Kaduna din watau Kaduna Market Traders Association (KMTA) a turance suma sun nesanta kan su da labarin inda suka ce suma ba da yawun su ba.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa kungiyoyi da dama dai a cikin yanayi na wani sabon salo, suna ta fitowa suna siyawa 'yan takara da dama fom din takara a zaben na 2019 dake karantowa.

A wani labarin kuma, Mun samu labarin cewa an tashi ba'a cimma matsaya ba a wani zaman sasanci da aka so yiwa 'yan takarar shugaban kasar Najeriya a karkashin inuwar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da wasu jiga-jigan jam'iyyar.

Kamar dai yadda muka samu, taron wanda aka gudanar a ofishin uwar jam'iyyar a garin Abuja ya samu halartar shugaban jam'iyyar ta PDP Cif Uche Secondus, gwamnonin jam'iyyar ta PDP da sauran jiga-jigan jam'iyyar.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel