Hukumar INEC tayi karin haske game da yiwuwar sake daga zaben 2019

Hukumar INEC tayi karin haske game da yiwuwar sake daga zaben 2019

- Hukumar INEC tayi karin haske game da yiwuwar sake daga zaben 2019

- Yace hukumar bata da wannan kudurin ko kadan

- Yace amma hukumar nada hurumin dagawar idan akwai dalilin yin hakan

Hukumar zabe mai zaman kan ta ta kasa watau Independent National Electoral Commission (INEC) a turance ta karin haske game da batun yiwuwar daga zabukan gama gari na shekarar 2019 da take shirin gudanarwa a shekarar 2019.

Hukumar INEC tayi karin haske game da yiwuwar sake daga zaben 2019

Hukumar INEC tayi karin haske game da yiwuwar sake daga zaben 2019
Source: Depositphotos

KU KARANTA: Gwamna Ambode yayi karin haske game da rikicin sa da Bola Tinubu

Kamar dai yadda muka samu, a cikin wata sanarwar da jami'in hulda da jama'a na hukumar, Mista Rotimi Oyekanmi ya sa wa hannu ya kuma rabawa manema labarai yace hukumar bata da wani kuduri na zahiri ko na boye na daga zaben mai zuwa.

Legit.ng ta samu cewa a cikin sanarwar, Mista Rotimi Oyekanmi ya kara da cewa wannan karin hasken ya zama dole ga hukumar musamman ma ganin yadda wasu jaridu suka buga labarin cewa wai shugaban hukumar yace za'a iya dage zaben.

Ya cigaba da cewa 'yan jaridar sun yiwa maganar shugaban hukumar mummunar fassara ne domin shi abun da yace shine kundin tsarin mulki ya baiwa hukumar damar daga zabe idan tana da yakinin cewa babu yanayi mai kyau kawai.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa a shekarar 2015 ma da ta gabata, hukumar zaben ta daga gudanar da zaben gama garin sakamakon rashin tsaro a wasu sassa na kasar, lamarin da ya jawo cece-kuce daga wasu 'yan kasar.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel