Matashi ya haye kololuwar karfen sabis domin nuna fushinsa a kan tabarbarewar tattalin arziki

Matashi ya haye kololuwar karfen sabis domin nuna fushinsa a kan tabarbarewar tattalin arziki

- Wani matashi, Nurudeen Iliyasu ya dare koluluwar karfin sabis a Abuja domin nuna bacin ransa game da tarbarbarewar tattalin arziki a Najeriya

- Iliyasu ya ce zai kwashe kwanaki bakwai a saman ba tare da ya ci abinci ba kuma bai damu ko zai rasa ransa ba

- Mai gadin karfen sabis din ya ce ya gargadi Iliyasu kada ya hau amma bayan ya tafi sai matashin ya sulale ya dare

Wani matashi mai shekaru 28, Nurudeen Iliyasu, ya haye kololuwar karfen sabis a babban birnin tarayya Abuja domin nuna bacin ransa a kan tabarbarewan tattalin arziki a Najeriya.

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ta ruwaito cewa an gano matashin a koluluwar karfen sabis a misalin karfe 12 na ranar Laraba a unguwar AYA da ke Abuja.

NAN ta kuma ruwaito cewa an ga fostoci da yawa a hanyar zuwa AYA masu dauke ta sakonni daban-daban da ke korafi kan halin da tattalin arzikin najeriya ta shiga a jikin karfen sabis din.

Matashi ya haye kololuwar karfen sabis domin nuna fushinsa a kan tabarbarewar tattalin arziki

Matashi ya haye kololuwar karfen sabis domin nuna fushinsa a kan tabarbarewar tattalin arziki
Source: Facebook

DUBA WANNAN: Dukkan 'yan takarar PDP sun hada kai a kan abu guda - Bafarawa

Mr Iliyasa ya ce sai ya kwashe kwanaki bakwai a koluluwar karfen domin a cewarsa a shirye ya ke ya sadaukar da rayuwarsa domin cigaban Najeriya.

Matashin ya ce zai cigaba da wannan zanga-zangar yunwar har na kwanaki bakwai domin ya nuna wa gwamnati bashin ransa domin ya yi kwanaki bai samu abincin da zai ci ba. Ya ce bai damu ba idan ya rasa ransa sakamakon matakin da ya dauka.

Matashi ya haye kololuwar karfen sabis domin nuna fushinsa a kan tabarbarewar tattalin arziki

Matashi ya haye kololuwar karfen sabis domin nuna fushinsa a kan tabarbarewar tattalin arziki
Source: Twitter

Iliyasu ya ce yana sana'ar sufuri ne da wasu buga-bugan amma abubuwa sun tsaya masa cak.

Mai gadin da ke kula da karfen sabis din, Mr Ayuba Luka, ya shaidawa NAN cewa ya gargadi Iliyasa kada ya hau karfen sabis din sai dai daga baya ya sulale ya hau ba tare da ya sani ba.

"Na ce masa kada ya hau karfen sabis din amma bayan na tafi ya sulale ya hau.

"Na yi mamakin ganinsa a koluluwar karfen yayin da na dawo, ya kira shugabani na domin su dauki matakin da ya dace," inji Ayuba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel