Za a daina dauke wutar lantarki idan Buhari ya sake zama shugaban kasa - Amaechi

Za a daina dauke wutar lantarki idan Buhari ya sake zama shugaban kasa - Amaechi

- Ministan zirga zirga, Rotimi Amaechi ya ce Nigeria zata daina samun matsalar daukewar wutar lantarki idan har aka sake zabar shugaban kasa Buhari

- Ya ce gwamnatin Buhari ta samu nasara a bangaren tsaro, yaki da cin hanci da rashawa, bunkasa noma da sufuri da sauransu

Ministan zirga zirga, Rotimi Amaechi a ranar Laraba ya ce gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta yi namijin kokarin farfado da tattalin arzikin kasar, ba wai a bangaren sufuri kadai ba.

Amaechi wanda ya bayyana hakan a Abuja a yayin wata tattaunawa da manema labarai dangane da ci gaban da ma'aikatarsa ta samu, ya ce gwamnatin Buhari ta samu nasara a bangaren tsaro, yaki da cin hanci da rashawa, bunkasa noma da sufuri da kuma kawo karshen rikicin makiyaya da manoma.

Ministan sufurin ya kuma ce Nigeria zata samu wutar lantarki awa 24 a kowace rana babu daukewa ma damar jama'a suka baiwa Buhari damar sake zama shugaban kasar a zaben 2019 da ke gabatowa.

KARANTA WANNAN: Tonon Silili: WAEC za ta bayyana sakamakon jarabawar wani dan takarar gwamna

Za a daina dauke wutar lantarki idan Buhari ya sake zama shugaban kasa - Amaechi

Za a daina dauke wutar lantarki idan Buhari ya sake zama shugaban kasa - Amaechi
Source: Depositphotos

"An samu ci gaba a bangaren samar da wutar lantarki. Mun matsa daga megawat 3000 zuwa 7000, amma ana rarraba megawat 5000 ne saboda wasu daga cikin kayayyakin rarraba wutar sun lalace, sai dai muna kan gyaran su a yanzu haka.

"Muna sa ran samar da wutar lantarki awanni 24 babu daukewa a kowace rana, amma dole ne sai an yi yan gyare gyare, don haka nike tunanin akwai bukatar sake bamu dama don ci gaba da shugabanci a 2019"

A cewar sa, abun takaici ne da rashin adalci idan aka ce ma'aikatar aiki ta kasa bata gudanar da wasu ayyukan azo a gani. An wofantar da titin zuwa Bonny bayan da mulkin Obasanjo ya kare, a lokacin an ware aiki titin akan kudi N39bn, amma a wannan gwamnati mai ci, an warewa aikin titin N12Obn wanda kuma za'a kammalashi akan lokaci.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel