Mayar da fam din takara: Buhari ya fadi dalilin da yasa ya ke neman tazarce

Mayar da fam din takara: Buhari ya fadi dalilin da yasa ya ke neman tazarce

- Shugaba Muhammadu Buhari ya ce yanke shawarar yin tazarce ne saboda cigada da kare hakokin 'yan Najeriya

- Shugaban kasa ya ce ba dai-dai bane a sake bawa wanda suka durkusa Najeriya damar sake dawowa mulki

- Shugaba Buhari ya kuma shawarci sauran 'yan jam'iyya da su cigaba da shirye-shirye domin ganin APC tayi nasara a 2019

Mayar da fam din takara: buhari ya fadi dalilin da yasa ya ke neman tazarce

Mayar da fam din takara: buhari ya fadi dalilin da yasa ya ke neman tazarce
Source: Instagram

A yau, Laraba ne Shugaba Muhammadu Buhari ya ce ya yanke shawarar sake tsayawa takara a shekarar 2019 ne saboda ya kare hakkin talakawan Najeriya.

Shugaban kasa ya yi wannan magana ne a yayin da ya tafi mayar da fom din takararsa a sakatariyar APC da ke Abuja, inda ya ce dole a hana wanda suka wargaza Najeriya daga 1999 zuwa 2015 dawowa mulki.

DUBA WANNAN: Babban malamin Islama na son a rage albashin 'yan siyasa

Ya kuma yi amfani da damar domin mika godiyarsa da kungiyoyin siyasa da suka yi masa karo-karo na N45.5 miliyan domin sayan takardan takarar zaben.

Ya ce, "Gani na taho tare da abokai da magoya baya domin in mika takardan neman takarar tikitin shugabancin kasa a 2019 karkashin inuwar jam'iyyar APC.

"Na yanke shawarar daukan wannan matakin ne saboda in kare hakokin dukkan 'yan Najeriya da yi musu hidima.

"Ina mika godiya da dimbin kungiyoyin da suka hada kudu domin saya min fom din takarar zabe. Ina tabbatar musu da sauran 'yan Najeriya cewa idan na samu tikitin takarar kuma na lashe zabe, zan cigaba da yiwa kasa hidima iya kokarina.

"Ina tunatar da sauran 'yan jam'iyya kada suyi barci, su cigaba da shirye-shiryen yadda za muyi nasara a zaben 2019.

"Ba zai yiwu mu kyalle wadanda suka durkusar da kasar daga 1999 zuwa 2015 su dare mulki su mayar da mu baya ba."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel