Hukumar soji tayi wani atisaye mai ban sha'awa a arewa maso gabas

Hukumar soji tayi wani atisaye mai ban sha'awa a arewa maso gabas

- A yanzu Sojin saman Najeriya sun zafafo

- Yaki da Boko Haram ya shekara goma ana gabzawa

- Sunyi wani sabon atisaye a Bauchin Yakubu

Hukumar soji tayi wani atisaye mai ban sha'awa a arewa maso gabas

Hukumar soji tayi wani atisaye mai ban sha'awa a arewa maso gabas
Source: Facebook

Hukumar sojin saman Najeriya, NAF, ta qaddamar da atisaye na kwana biyar dags jiya, a jihar Bauchin Yakubu dake arewa maso gabashin Najeriya.

Atisayen, zai koyawa sojoji yadda zasu iya kwaso wadanda ke da raunika a lokutan yaki da ta'addanci wanda yakici yaki karewa a yankin.

Kokarin sojin dai shine su samar da sabbin hanyoyin iya tafiyar da yakin bisa kwarewa da zamananci, wanda shine hangen babban kwamandan sojin saman, Air Marshal Sadique Abubakar.

Sai dai kuma, ana ganin an gagara samarwa yankin zaman lafiya ya zuwa yanzu. Su kuma mayakan sai sake fidda hanyoyin fidda jama'a daga yankunansu.

DUBA WANNAN: Buhari zai kuma ciwo bashi daga Japan

Wannan dai lokacin zabe ne, kuma an kula itama kungiyar Boko Haram ta kara kaimi wajen kisan jama'a da ma sojojin kasar nan, lokacin da hankalin 'yan siyasa ya koma sama.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel