Matasa a Kwara sun shirya gangamin nuna goyon bayan Saraki ya zama shugaban kasar Nigeria

Matasa a Kwara sun shirya gangamin nuna goyon bayan Saraki ya zama shugaban kasar Nigeria

- Wata kungiyar matasa a jihar Kwara, ta shirya gudanar da wani gangamin nuna goyon bayan su ga kudirin Saraki na tsayawa takarar shugaban kasa

- Mr. Olanrewaju Oba ya ce taron zai kasance cike da murnar irin ayyukan alkairin da Bukola Saraki ya kawo a lokacin da ya ke shugabancin jihar

- Za'a fara gangamin da misalin karfe 7 na safiyar ranar Asabar, 12 ga watan Satumba, daga mahadar titin Ibrahim Taiwo, a Ilorin, jihar Kwara

A ci gaba da kokarin nunawa duniya irin karbuwar da Sanata Bukola Saraki ya yi a mahaifarsa dama jiharsa baki daya, wata kungiyar matasa da ke jihar Kwara, ta shirya gudanar da wani gangamin nuna goyon bayan su ga kudirin Saraki na tsayawa takarar shugaban kasa, a ranar 15 ga watan Satumba.

Da ya ke jawabi ga manema labarai a ranar Laraba a Ilorin, shugaban kungiyar, Mr. Abdulmajeed Olanrewaju Oba, ya ce gangamin ya zama wajibi ne duba da irin ayyukan alkairin da Saraki ya kawowa jihar a lokacin da ya ke matsayin gwamna da kuma yanzu da ya ke shugabantar majalisar dattijai ta kasa.

Mr. Olanrewaju Oba ya ce: "Wannan taron zai kasance cike da murnar irin ayyukan alkairin da Bukola Saraki ya kawo a lokacin da ya ke shugabancin jihar, wannan taro zai nunawa duniya irin soyayyar da muke masa.

KARANTA WANNAN: Yan bindiga sun kashe Sajen na yan sanda tare da warewa da bindigarsa a Owerri

Matasa a Kwara sun shirya gangamin nuna goyon bayan Saraki ya zama shugaban kasar Nigeria

Matasa a Kwara sun shirya gangamin nuna goyon bayan Saraki ya zama shugaban kasar Nigeria
Source: Facebook

"Za'a fara gangamin ne da misalin karfe 7:00 na safiyar ranar Asabar, 12 ga watan Satumba, daga mahadar titin Ibrahim Taiwo, dai dai kusa da shagon Mr Biggs, a Ilorin, jihar Kwara.

"Muna bukatar duk wanda zai halarci wannan gagarumar zanga zanga, to ya sanya bakin wando tare da kalar rigar da yaga dama" a cewar sa.

Da ya ke karfafa guiwar yan siyasa a kasar na kwaikwayon irin salon shugabanci na shugaban majalisar dattijai ta kasa, shugaban kungiyar ya ce matasan Kwara na goyon bayan kudirin Saraki na zama shugaban kasar Nigeria.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Tags:
Mailfire view pixel