Tabbas Buhari zai yi karin albashi – Fadar shugaban kasa

Tabbas Buhari zai yi karin albashi – Fadar shugaban kasa

- A yau, Laraba, fadar shugaban kasa ta bayar da tabbacin cewar shugaba Buhari zai yi karin albashi

- Mai bawa shugaba Buhari shawara a kan harkokin da suka shafi majalisar dattijai, Ita Enang, ne ya sanar da hakan

- Enang ya bayar da wannan tabbaci ne yayin kare gwanatin Buhari a kan zargin cewar ta ki cewa komai a kan batun Karin albashi

A yau, Laraba, ne fadar shugaban kasa ta bayar da tabbacin cewar shugaba zai yiwa ma’aikata Karin albashi.

Mai bawa shugaba Buhari shawara a kan harkokin da suka shafi majalisar dattijai, Ita Enang, ne ya tabbatar da hakan ga kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) yayin da yake mayar da martini a kan zargin cewar gwamnatin Buhari ta yi burus da batun karin albashin.

Tabbas Buhari zai yi karin albashi – Fadar shugaban kasa

Buhari
Source: Depositphotos

An dade ana bukatar gwamnatin tarayya tayi karin albashi ga ma’aikatanta musamman ganin yadda rayuwa ke kara tsada a Najeriya. An mayar da mafi karancin albashi a Najeriya N18,000 a shekarar 2011, shekaru 8 kenan da suka gabata.

Ina son sanar da ‘yan Najeriya cewar gwamnatin shugaba Buhari gwamnati ce ta gaskiya dake da niyyar inganta albashin ma’aikata.

DUBA WANNAN: Takanas-ta-kano: Gwamnan APC ya ziyarci Kano don yiwa Shekarau murnar fita daga PDP

“Da shugaba Buhari bashi da niyyar yin karin albashi da tun farko ba zai kafa kwamitin neman gyara albashin ma’aikata karkashin jagorancin shugabar hukumar ma’aikata ba. Ministan kwadago ma na cikin kwamitin,” a kalaman Enang.

A ranar Litinin ne shugaban kungiyar kwadago na kasa, Ayuba Wabba, ya zargi gwamnatin tarayya da yiwa batun karin albashin daukar sakainar kasha.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel