Najeriya na bukatar shugaban kasa mai tafiya da zamani - Saraki

Najeriya na bukatar shugaban kasa mai tafiya da zamani - Saraki

- Shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki yace kasar na bukatar Shugaba mai tafiya da zamani

- Saraki dai na neman takarar kujerar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP a zabe mai zuwa

- Yana cigaba ne da rangaji domin neman goyon bayan mambobin jam'iyyar kafin zaben fidda gwani

Dan takaran kujerar shugaban kasa kuma shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki a ranar Laraba, 12 ga watan Satumba ya bayyana cewaa Najeriya na bukatar shugaban kasa da mai tafiya da zamani.

Saraki, wadda ya ziyarci Gwamna Ben Ayade na jihar Cross River domin neman goyon bayansa a kudirinsa na zama shugaban kasa a zabe mai zuwa yace Najeriya na muradin shugabanci mai tafiya da sauyin lokaci.

Najeriya na bukatar shugaban kasa mai tafiya da zamani - Saraki

Najeriya na bukatar shugaban kasa mai tafiya da zamani - Saraki
Source: Depositphotos

“Na kasance a Cross River domin neman goyon bayan diliget a zaben fidda gwani na jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP) mai zuwa. Ina da ake bukata wajen shugabanci mai inganci wannan ne yasa nake neman goyon bayan dukkanin yan Najeriya domin cimma wannan buri.” Inji shi.

Gwamna Ben Ayade ya yabama Saraki kan fitowa da yayi yana neman takarar kujerar Shugaban kasa, inda ya kara da cewa yana da duk abunda ake bukata don daukaka kasar Najeriya.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa tsohon gwamnan jihar Kano kuma dan takarar kujerar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Dr. Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana cewa chanjin da shi da sauran wadanda suka marawa Shugaban kasa Muhammadu Buhari baya suka bi a 2015 shine babban kuskuren da suka yi.

KU KARANTA KUMA: Tafiyar chanjin 2015 babban kuskure ne - Kwankwaso

Ya bayyana hakan a ranar Laraba, 12 ga watan Satumba da yake jawabi ga yan PDP na jihar Niger da magoya bayansu a sakatariyar jam’iyyar dake Minna cewa yawan Magana da aka tayi akan chanji ai kawo komai ba face yunwa, kashe-kashe da kuma rashin aiki.

Da yake Magana akan batun tsayar da dan takara guda da shugabannin jam’iyyar sun nema, Kwankwaso ya bayyana cewa ba zai amince da hakan ba amma duk wanda yayi nasarar lashe zaben fidda gwani zai samu cikakken goyon bayansa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel