2019: Doyin Okupe ya dawo aikin da ya fi iyawa, sayar da dan takarar PDP

2019: Doyin Okupe ya dawo aikin da ya fi iyawa, sayar da dan takarar PDP

- Okupe ne shugaban kamfen din Saraki na kafafen yada labarai

- Muhammad Wakil, shugaban kamfen din Saraki ne ya sanar da hakan

- Ya taba yin babban mai bada shawara akan harkokin sadarwa ga Obasanjo da Goodluck

2019: Doyin Okupe ya dawo aikin da ya fi iyawa, sayar da dan takarar PDP

2019: Doyin Okupe ya dawo aikin da ya fi iyawa, sayar da dan takarar PDP
Source: Depositphotos

Shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki ya zabi Doyin Okupe, tsohon mai taimakon Goodluck Jonathan, a matsayin shugaban kungiyar yakin neman zaben shi na kafafen yada labarai.

Saraki dai na neman kujerar shugabancin kasa a karkashin inuwar jam'iyyar PDP.

Muhammad Wakil, daraktan yakin neman zaben Saraki, shi ya sanar da hakan.

Wakil yace "Okupe zai yi aiki da sauran kwararrun kungiyar domin sanar da yan Najeriya da ma duniya baki daya."

DUBA WANNAN: INEC bata da laii, majalisa ce - Hadimin Buhari

Okupe, likita ne kuma Dan siyasa, ya taba yin sakataren watsa labarai a tsohuwar jam'iyyar NRC, Daraktan sadarwa ga shugaban kasa Olusegun Obasanjo da Goodluck Jonathan kuma yayi babban mai bada shawara akan kafofin yada labarai ga shuwagabannin kasar biyu"

Okupe ya bar jam'iyyar PDP a shekarar da ta gabata, yace jam'iyyar bazata haifa da mai ido ba a nan gaba.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel